✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu sarautar gargajiya na da muhimmanci wajen samar da tsaro – Hakimin Darufai

Alhaji MuhammaduUsnam Barkabali wanda aka fi sani da Maigona tsohon soja ne wanda ya yi aiki da tsofaffin shuganannin kasa na soja Janar Yukubu Gowon,…

Alhaji MuhammaduUsnam Barkabali wanda aka fi sani da Maigona tsohon soja ne wanda ya yi aiki da tsofaffin shuganannin kasa na soja Janar Yukubu Gowon, marigayi  Murtala Muhammed, marigayi Janar Shehu Musa Yar’adau. Yanzu shi ne Hakimin Darufai da ke karamar Hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba. Ya yi bayanai masu yawa wadanda suka shafi yadda abubuwa ke tafiya a kasar nan a hira da wakilin Aminiya:

 

A matsayinka na tsohon soja wanda ya yi aiki da manyan hafsoshin soja har tsofaffin shuwagabanin kasa na soja, ya kaga yadda kasar nan take a yanzu?

Akwai bambanci tsakanin yadda ala’amura suke a da da yanzu a kasar nan. A da akwai hadin gwiwa tsakanin jama’ar kasar nan musamman ’yan Arewa kuma jama’a na yi wa gwamnati biyayya amma yanzu abin ya canja. Kuma babbar matsalar kasar nan ita ce yadda kowa ya sa ido kan kudi, ana yin aikin gwamnati ba don kishin kasa ba, sai don abin da za a samu.

Me za ka ce kan kiraye-kiraye da jama’a ke yi na a sanya sarakunan gargajiya cikin tsarin mulki Najeriya.

Wannan ya dace sosai, da farko kowa ya san cewa sarakuna su ne iyayen al’umma, kuma suna da muhimmiyar gudunmawa da za su bayar wajen kawo ci gaban kasa tare da samar da zaman lafiya. Kafin tsarin Dasuki wato “Dasukoreform”, tsarin da ya mayar da sarakuna a matsayin shuwagabanin gargajiya ya karbe kotuna da gidajen yari daga hannun sarakuna, kowa ya san cewa sarakuna sun bayar da gudunmawarsu ta  hanyoyi  da dama.

Kuma a da dukkan wani bako da ya zo gari gidan mai anguwa ko dagaci zai sauka. Wannan tsari ya sa  sarakuna sanin dukan wani bako da yake zaune a masarautarsu, ta haka ne sarakuna ke sa ido a kan jama’ar da ke zaune a yankinsu. Bayan wannan kuma sarakuna sun bayar da gudunmawa ta fuskar ayyukan noma da ilimi da.

Kuma matsalar Boko Haram da masu sace mutane don karban kudin diyya, sun faru ne saboda rashin sa ido kan yadda mutane ke kaura daga wannan wuri zuwa wancan ba tare da sanin hukuma ba.

Kaga in an bai wa saraukuna wata dama a hukumance, za a sa ido kan wannan lamarin.

In ka dubi yadda hukuma ke sa ido ga kowa da kowa a kasashen Turai da Amurka ya sha banban da yadda ake barin jama’a ke zaune a wurare ba tare da hukuma ta sani ba.

Akwai  matsalar tabarbarewar tarbiya a tsakanin matasa musamman a nan yankin Arewa, me ya haifar da wannan matsala?

Dalilan na da yawa, na farko dai iyaye sun bar nauyin da ya dogara a kansu na bayar da tarbiya mai kyau ga ’ya’yansu sai kuma ita kanta al’ummar. Iyaye a yanzu da yawa saboda son ’ya’ya basa sa ido a kan yadda ’ya’yansu ke gudanar da rayuwarsu.

Sai kaga yaro na yin wasu halaye amma iyaye saboda sonsu, sai kaga sun kyalesu. Amma a da uba baya kawar da idonsa in ya ga dansa na yin wasu abubuwa wadanda suka sabawa tarbiya ta gari.

Kuma ga matsalar finafinai na banza tare da wayar hannu wadanda dukansu suna gurbata tarbiyar matasa. Saboda haka, ya kamata iyaye su sa ido matuka kan ‘ya’yansu kuma su mai da hankalinsu wajen bai wa ‘ya’yansu ilimi na addini da na zamani.

Dole ne iyaye su mai da hankalinsu wajen koya wa ’ya’yansu sana’ar hannu tare da basu karfin gwiwa kan neman ilimin addini da na zamani. Ta wannan hanyar matasanmu za su daina zaman banza su rungumi sana’o’i.

Kamar yadda kowa ya sani ne duk wanda bai da aikin yi to zai iya shiga ayyukan banza da aikata laifuka. Wannan matsala na rashin sana’a ita ce ta sa ’yan siyasa a Arewancin kasar nan ke amfani da ’ya’yan talakawa wajen bangan siyasa. Sai ka ga yaran talakawa na kashe kansu da sunan bangan siyasa amma ’ya’yansu na karatu a jami’o’i da ke kasashen waje kuma aiki mai kyau na jiransu in sun kammala makaranta.

In sun in fada maka cewa ni ina da ’ya’ya sama da arba’in wadanda suka hada maza da mata, kuma 30 daga cikinsu sun kammala karatun jami’a. wannan ya nuna cewa na mai da hankali wajen ganin cewa na ba su ilimi.

Haka ya kamata dukan iyaye su yi, su maida hankali sosai wajen bai wa ’ya’yansu ilimi na addini da na zamani. In haka ya samu, za a sami yara na gari wadanda za su kasance shuwaganin na kwarai a gaba.

Awancan lokaci da na kowa ne, hakkin tarbiyar da matasa ba a kan iyaye kadai ya rataya ba, yana kan al’umma ne baki daya. kuma akwai bukatar jama’a su taimaka wa marayu su dauki nauyin karatunsu da bukatunsu na yau da kullum kafin su girma.

An samu matsalar rashin jituwa tsakaninka da ’yan uwanka a kan wannan matsayi wanda yanzu Gwamna Darius Ishaku ya tabbatar maka mai zaka fadi game da hakan? 

Na ji dadi kwarai kan yadda shi mai girma gwamna ya tabbatar mani da wannan sarauta na hakimin Darufai, dama sarautar tamu ce.

Zan yi iyakacin kokarina ta fuskar hada kan ’yan uwan da daukacin jama’a don ganin an sami zaman lafiya da ci gaba a masarautar Darudai.

Kasan cewa sai da zaman lafiya ne za a sami ci gaba, ina sun in yi amfani da wannan dama in yi kira ga daukacin jama’ar masarautata da su bani cikakken hadin kai don a sami ci gaba mai dorewa a wannan yankin na Darufai.

Mai ya baka karfin gwiwa wajen mayar da hankali wajen gudanar da aikin gona? 

Ai mu jama’ar Arewacin kasar nan noma ya kasance babban sana’a a gare mu kuma gashi gwamnatin Tarrayya da ta Jihar Taraba  sun mai da hankali wajen bunkasa wannan babban sana’a wanda a halin yanzu an samu gagarumar nasara ta fuskar noma a wannan jiha da kasa baki daya.

To, mu a matsayinmu na shuwagabannin al’umma, ya zama tilas mu rungumi wannan sana’a domin karfafawa jama’a gwiwa su rungumi aikin gona.

Kuma kowa ya san cewa aikin noma na da muhimmanci ta fuskar tattalin arzikin kasa. Wanda ya nuna a fili cewa duk kasar da tafi karfin abincin da jama’arta za su ci, to wannan kasa ta samu ci gaba mai kyau.

Sabo da haka wannan tsari da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo na cewa jama’a su kama aikin noma ya yi daidai.

Akwai matsalar tsaro a kasa sosai, a ganinka wani taimako ne sarakuna za su iya bayarwa don shawo kan wannan matsala?

Ai na fada tun da farko cewa akwai bukatar a koma tsarin da, inda sarakuna ke da muhimmanci ta fuskar zamantakewar al’umma. Ina nufin sarakuna a basu hakkinsu na shuwagabannin jama’a a hukumce.

Kaga in aka yi haka, sarakuna za su sami damar sa ido sosai a kan jama’ar da suke zaune a yankunansu kuma zai zama tilas sarakuna su san jama’ar da suke zaune a masarautarsu. Ta haka duk bakon da ya shigo zai zama dole ya kai kansa ga mai anguwa wanda shi ne wakilin Dagaci, shi kuma Dagace wakilin Hakimi ne, haka abin zai kasance hukuma ta san da zaman kowanne irin mutane da ke zaune a kasa ba yadda yake kara zube a yanzu ba.

Wannan tsari zai taimaka wajen tunkarar matsalar tsaro domin so da yawa mutane na zaune a wuri, amma sarakuna ba su san da zamansu ba sai sun aikata wani laifi a ce za a fara bincike.