✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu satar kayan Kamfanin MTN sun shiga hannun ’yan sanda

Wadansu mutum uku da ake zargi da kwarewa wajen barna da satar kayayyakin kamfanonin sadarwa a ’yankin Ibafo a Jihar Ogun sun shiga hannun ’yan…

Wadansu mutum uku da ake zargi da kwarewa wajen barna da satar kayayyakin kamfanonin sadarwa a ’yankin Ibafo a Jihar Ogun sun shiga hannun ’yan sanda bayan da wani mai gadin turken na’urar Kamfanin MTN  a yankin Papa Ibafo ya shigar da koke a ofishin ’yan sandan ’yankin.

Mai gadin ya ce, ’yan fashi sun dirar wa wajen sun kwashe batira da kudinsu da ya kai Naira miliyan daya da dubu 800, lamarin da ya sanya Baturen ’Yan sandan Ibafo DPO Abiodun Ayide da jama’arsa suka tunkari ’yan fashin wadanda suka watsar da abin da suka sata suka arce da gudu sai dai ’yan sandan sun yi nasarar kama mutum daya a cikinsu mai suna Adeola Oyesanya wanda ya bada bayanan da aka kai ga kama ragowar mutum biyu da ke sayen kayan da suka sato.

Mai magana da yawun rundunar ’Yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewa wadanda ake zargin sun hada da: Adeola Oyesanya da  Bashiru Mohammed sai Musa Mohammed, kuma duk sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa abin da suka ce sun dade suna yi, ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar Kenneth Ebrimson, ya bada umarnin tura wadanda ake zargin sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da su a kotu domin su fuskanci hukunci.