✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu satar mutane sun hallaka Limamin Juma’a

Imam Gambo Mohammed Abubakar na daya daga cikin limaman da Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah ke ji da su a Jihar Taraba, musamman kan kokarinsa na…

Imam Gambo Mohammed Abubakar na daya daga cikin limaman da Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah ke ji da su a Jihar Taraba, musamman kan kokarinsa na gudanar da da’awar Musulunci a sassan jihar.

Limamin mai kimanin shekara 48 ya gamu da ajalinsa a ranar Lahadi 27 ga Oktoban bana  yayin da ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka harbe shi a kan hanyarsa ta zuwa Jalingo daga garin Iware kimanin kilomita 24 daga garin Jalingo.

Aminiya ta gano yadda lamarin ya faru har ya kai ga kashe malamin da wani matukin Keke NAPEP.

Kamar yadda wakilin Aminiya ya gano, Imam Gambo ya shiga motar haya ce daga garin Iware zuwa gida Jalingo, kuma suna cikin tafiya sai direban motar ya hangi ’yan bindigar sun tsare hanya suna ta harbin motoci.

Ganin haka sai direban ya taka birki ya nemi ya juya ya koma inda suka fito amma sai ’yan bindigan suka bude musu wata inda harsashi ya samu Imam Gambo.

Majiyarmu ta ce direban motar bai ma san harsashi ya samu Imam Gambo ba domin kaduwa da tsorata da dukkan fasinjojin motar da shi kansa direban suka yi.

Dan marigayin ne ya gane cewa an harbi mahaifinsa domin ya ji yana cewa, “Inna lillahi wa inna illaihun raji’un” tare da yin kalmar shahada.

Majiyar da ke kusa da marigayin ta shaida wa Aminiya cewa kafin direban ya isa wani kauye da ake kira Sibire da bai da nisa da inda ’yan bindigar suka harbi limamin har ya rasu.

Na’ibin Imam Gambo mai suna Malam Musa Yusuf ya shaida wa wakilinmu cewa Imam Gambo ya fito ne daga wani kauye mai suna Hamma-Hamza kusa da garin Iware inda ya yi noman masara kan hanyarsa ta komawa gida.

Ya ce marigayin ya kusan shafe mako daya a kauyen Hamma-Hamza domin ana yin  masa girbin masara. Ya ce Imam Gambo ya kasance duk shekara yana noma amma bana ne ya yi gona a wancan kauyen na Hamma-Hamza.

Da yake magana dangane da kashe Imam Gambo, Shugaban Limaman Kungiyar Izala a Jihar Taraba, Imam Barkindo ya nuna matukan juyayi kan kisar da ’yan bindigar suka yi wa Imam Gambo.

Ya ce Imam Gambo na daya daga cikin limaman da kungiyar Izala a Jihar Taraba ke alfahari da su saboda himmarsa da kokarinsa wajen aikin da’awa.

Imam Barkindo ya ce duk da kasancewar marigayi Imam Gambo shi ne limamin Masallacin Juma’a na Unguwan Kasa a garin Jalingo ya kasance a lokacin rayuwarsa yana gudanar da wa’azi a masallatai daban-daban a ciki da wajen garin Jalingo.

Ya ce a lokutan watan azumi kungiyar ta rika tura shi wurare daban-daban a jihar don gudanar da tafsiri.

Ya ce tunda aka gina Babban Masallacin Juma’a na Izala bangaren Kaduna a garin Jalingo ba a taba hada al’ummar Musulmi masu yawa waje wata jana’iza ba kamar yadda jama’a  suka hallara a wajen jana’izar marigayi Imam Gambo.

Ya ce marigayin ya rasu ya bar mata da ’ya’ya bakwai maza hudu da mata uku kuma Kungiyar Izala za ta dauki nauyin ci gaba da karatun marayun da ya bari.

Ya nuna taikaci kan gazawa tare da nuna halin ko in kula da Gwamnatin Jihar Taraba da jami’an tsaro ke yi kan abubuwan da suke  faruwa a kan hanyar Jalingo zuwa Mutum-Biyu musamman kusa da sansanin horar da masu yi wa kasa hidima (NYSC).

Imam Barkindo ya ce kusan shekara daya ke nan masu garkuwa da mutane da ’yan fashi da makami ke cin karansu ba babbaka a wannan wuri da aka hallaka Imam Gambo amma an kasa daukar wani mataki wajen magance matsalar.

Bincike ya nuna a daminar bana masu garkuwa da mutane sun sace tare da hallaka manoma masu yawan gaske a sassan Jihar Taraba wanda hakan ya hana manoma zuwa noma a gonakinsu don gudun kada a sace su.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba DSP Dabid Misal ya tabbatar da kashe Imam Gambo tare da wani mutum daya da ’yan bindigar suka yi a hanyar Jalingo zuwa Mutum-Biyu.

Ya ce ’yan sanda sun kuma kubutar da mutum bakwai da ’yan bindigar suka sace a daidai wajen da aka kashe Imam Gambo.