Search
Subscribe
Masu sayar da sababbin Naira sun shiga hannun ’yan sanda a Legas

Masu sayar da sababbin Naira sun shiga hannun ’yan sanda a Legas

Rudunar ’Yan sandan Jihar Legas ta kama wadansu mutum takwas da ake zargi da cinikin kudin sababbin takardun Naira da akasari ake amfani da su a wuraren biki.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa jami’an  rundunar tare da hadin gwiwar jami’an Babban Bankin Najeriya (CBN) ne suka kama wadanda ake zargin wadanda ke hada-hadar sababbin nairori a wata kasuwa a yankin Ikeja, inda suka same su da sababbin nairori na Naira miliyan  2 da dubu 445 da 550 a ranar Juma’ar da ta gabata. Ya ce wadanda aka kama sun hada da Adetoro Adijat mace mai shekara  37 da Mahmoud Ayoola dan shekara 42 sai  Eze Madu dan shekara 27 da  Olorunfunmi Shakirat ’yar 38 sai  Akonji Julius dan shekara 40 da  Olalekan Kadri mai shekara 23 da  Akinsonya Abiodun dan shekara 34 sai  Adeniyi Yetunde mai shekara 30, “Za mu gurfanar da su a kotu domin su fuskanci shari’a saboda laifin da ake zarginsu ya saba wa  dokar Babban Bankin Najeriya sashi na 20 da  21 na shekarar 2007. Ya ce hukuncin da za su fuskanta zai zamo zaman gidan yari na tsawon wata shida ko tarar da ba za ta gaza Naira dubu 50 ba, in aka same su da laifi.  Ya kamata jama’a su sani lika kudi ko sayar da sababbin takardun kudi abu ne da dokar kasa ta hana,”  inji DSP Elkana.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin