Daily Trust Aminiya - Masu sukar gwamnatin Yobe su gwada abin da ta Tarayya ta yi
Subscribe

Masu sukar gwamnatin Yobe su gwada abin da ta Tarayya ta yi a jihar – Fema

Wani kusa a gwamnatin Jihar Yobe Alhaji Sani Fema ya kalubalanci ’ya’yan Jam’iyyar PDP da ke zargin gwamnatin Alhaji Ibrahim Gaidam na Jam’iyyar APC cewa ba ta yi wani aikin a zo a gani don inganta rayuwar al’ummar jihar ba, kan su nuna su irin ayyukan da gwamnatinsu ta Tarayya a karkashin PDP ta yi wa al’ummar jihar Yobe da na kasa baki a sama da shekara 15 da ta yi tana mulkin kasar nan.
 Alhaji Sani Fema ya yi wannan kalubale ne a tattaunawarsu da Aminiya a Damaturu don mayar da martani kan zargin da kusoshin PDP a jihar ke yi cewa babu wani aikin azo a gani na inganta rayuwar al’umma da gwamnatin Gaidam take yi in ban da cin kudi.
Ya ce Gwamna Gaidam ya yi tasa ya kuma yi tasu, domin ba ya ga aikin da ya wajaba ya yi, yana aikin da ya wajaba Gwamnatin Tarayya a karkashin Jam’iyyar PDP ta yi ne kamar gina hanyar Damaturu zuwa Buni Gari da karasa aikin hanyar Baimari zuwa Maino Saruwa a Jamhuriyar Nijar.
Ya kara da cewa irin wannan zargi da ’yan adawa ke yi ga gwamnatin jihar Yobe a da ma bai yi komai ba, ballantana yanzu da ruwa ke shirin karewa dan kada musammam ganin cewa al’ummar kasa na shirin yin waje da PDP a zaben 2015, saboda irin mulkin malaka’un da take yi, tare da fatar jam’iyyar ceton al’umma ta APC ta fitar da su daga kangin fatara da talauci da rashin tsaro.
Alhaji Sani Fema ya ce duk da yadda Jihar Yobe ke fama da tabarbarewar harkokin tsaro, hakan bai hana Gwamna Ibrahim Gaidam gudanar da ayyukan raya kasa fiye da wasu jihohin da ba su fuskantar irin wannan matsala ba.
Ya ce dole ne a jinjina wa mahukuntar jihar kan kokarin da suke yi na inganta rayuwar al’umma, musamman a fannin tsaro inda jihar ta kashe kusan Naira miliyan 280 ga jami’an tsaro, ban da sayo daruruwan motocin sintiri don saukaka musu a yakin da suke yi da masu tada zaune-tsaye. 

texem
More Stories