✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu zanga-zanga a Haiti sun nemi Shugaban kasa ya sauka

A Litinin da ta gabata ce wasu dubban masu zanga-zanga a kasar Haiti suka yi taho-mu-gama da ’yan sanda, a yayin da suke kira ga…

Masu zanga-zanga a Haiti, suna kona tayoyi a kan titiA Litinin da ta gabata ce wasu dubban masu zanga-zanga a kasar Haiti suka yi taho-mu-gama da ’yan sanda, a yayin da suke kira ga Shugaban kasar, Michael Martelly da ya sauka daga mulki.
A ’yan kwanakin nan dai kasar Haiti ta fuskanci zanga-zanga da tarzoma a yankuna daban-daban, a sanadiyyar koke-koken da al’ummar kasar suke game da tsadar rayuwa. Haka kuma al’ummar suna kokawa da masu mulkinsu, cewa almundahana da sace-sacen dukiyar gwamnati sun yi yawa.
A nasa bangaren, Shugaban kasa Martelly ya roki al’ummar kasar da su hada kai domin ceto kasar daga talaucin da ke addabar ta.
Shugaban ya dare mulki ne shekaru biyu da suka gabata, inda ya yi alkawarin sake gina kasar da gina tattalin arzikinta, bayan da girgizar kasa ta daidaita kadarorin al’umma a 2010.
A Litinin din da ta gabata, an ga dubban masu zanga-zanga suna kona tayoyi tare da kare hanyoyi a babban birnin kasar, suna ambata cewa lallai sai Shugaban kasar ya sauka nan take, domin kuwa a cewarsu, ya gaza a mulkinsa.
“Muna yin iyaka kokarinmu domin ganin mu cire shugaban daga mulki kuma ba za mu sarara ba har sai ya sauka.” Inji Jean Daniel, daya daga cikin dubban masu zanga-zangar, a yayin da yake magana da kamfanin dillacin labarai na AP.
An samu rahoton cewa dubban masu zanga-zangar sun rika jifar ’yan sanda da duwatsu, a yayin da su kuma suka rika mayar da martani da barkonon tsohuwa.