✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Masu zanga-zanga sun daka wa kayan tallafin COVID-19 wawa

Mazauna Osogbo, babban birnin jihar Osun sun daka wawa a wani rumbun ajiye kayan abinci da Gwamnatin Tarayya ta ba jihar a matsayin tallafin COVID-19.…

Mazauna Osogbo, babban birnin jihar Osun sun daka wawa a wani rumbun ajiye kayan abinci da Gwamnatin Tarayya ta ba jihar a matsayin tallafin COVID-19.

A ranar Juma’a dandazon jama’a sun yi wa ma’ajiyar da ke kamfanin CPI a Ede tsinke tare da kwashe kayan abinci daga cikinta.

An hangi mutanen na ta jidar kayan da suka hada da shinkafa, taliya da dai sauransu ba tare da shamaki ba.

Sai dai yunkurin jin ta bakin gwamnatin jihar kan lamarin ya ci tura sakamakon kin daukar wayarmu.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton mutane na ci gaba da yin tururuwa sun dibar kayan.

A halin da ake ciki zanga-zangar #EndSARS na ci gaba da gudana a sananniyar unguwar nan ta Olaiya da ke birnin na Osogbo.

Gwamnatin jihar dai ta janye dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta sanya a a ranar Laraba.