✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu zanga-zanga sun jefi tawagar gwamnoni a Jihar Ribas

Ranar Talata ’yan zanga-zangar nuna adawa ga gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi suka jefi tawagarsa da ta gwamnoni hudu da suka ziyarce shi a Fatakwal…

Ranar Talata ’yan zanga-zangar nuna adawa ga gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi suka jefi tawagarsa da ta gwamnoni hudu da suka ziyarce shi a Fatakwal don nuna goyon bayansu gare shi.  
Tun farko masu zanga-zangar sun mamaye filin jirgin na Fatakwal kafin gwamnonin su isa.  Gwamnonin kuwa su ne na Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido na Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da na Adamawa, Admiral Murtala Nyako da kuma na Neja, Alhaji Mu’azu Babangida Aliyu, wanda shi ne shugaban majalisar gwamnonin jihohin Arewa.
Bincike ya nuna an kai matasan masu zanga-zangar a cikin bas-bas 20 tun misalin karfe bakwai na safe a yayin da aka ji kishin-kishin din zuwan gwamnonin.
Matasan sun gudanar da zanga-zangar ce kuwa a karkashin lemar wata kungiya ta Grassroots Debelopment Initiatibe, inda suka tare sassan zuwan baki a filin jirgin, suna dauke da kwalayen da aka yi rubuce-rubucen batunci ga gwamnan jihar da kuma goyon bayansu ga Shugaba Jonathan a zaben shekarar 2015.
Gwamna Amaechi ya isa filin jirgin na Fatakwal daga Abuja kafin zuwan bakin nasa, inda ya zauna a sashen karbar baki na manyan mutane.  Yayin da gwamnonin suka isa, sai suka shiga jerin gwanon motoci zuwa gidan gwamnati, inda matasan suka fara jifar su da ruwan leda da duwatsu da sanduna da kuma ruwan roba, sai da tawagar ta isa gidan gwamnati ba tare da an sami wata tirka-tirka mai tsanani ba.  Suna isa gidan gwamnati kuwa, sai suka shiga wani dakin taro suka kulle.
Kwamishinar watsa labarai ta jihar, Misis Ibim Seminitari ta yi tir da abin da ya auku, ta nuna ’yan adawa da gwamnatin Gwamna Amaeci ne suka shirya shi. Ta bayyana cewa an fasa wata bas da kwamishinoni suka shiga zuwa filin jirgin saman, ba don halin dattaku da gwamnan ya nuna ba da an yi kare-jini-biri-jina da magoya bayansa da masu zanga-zangar.
Lokacin da wakilinmu ya tuntubi kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Ribas din, Angela Agabe a waya don jin ta bakinta game da lamarin ba ta amsa kiransa ba.