Aminiya

Masu zanga-zanga sun mamaye ginin majalisa

Wadansu masu zanga-zanga sun mamaye ginin Majalisar Dokoki da ke Abuja,inda suke kiraye-kirayen murabus din Shugaban Majalisar Dattawa Dokta Bukola Saraki.

ADVERTISEMENT

Kotun Da’ar Ma’aikata tana tuhumar Saraki ne da zargin aikata laifuka 13 wadanda ke da alaka da yin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Har ila yau, masu zanga-zanga sun bukaci sanatocin nan guda 36 da suka karbi manyan motocin alfarma da su gaggauta dawo da su, ko su fuskanci fushin ‘yan Najeriya.

ADVERTISEMENT

Sun fara zanga-zangar ne yau (Talata) daga Dandalin Unity Fountain da ke Abuja da misalin karfe 11:00 na safe.