Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mata 28 suke takarar majalisar dokokin Jihar Filato

Akalla mata 28 a karkashin jam’iyyu daban-daban ne suke neman takarar majalisar dokokin Jihar Filato.
A cikin wata takarda mai dauke da sunayen ‘yan takarar majalisar dokokin Jihar Filato da Hukumar zave ta INEC ta fitar a makon jiya Aminiya ta gano mata ‘yan takara za su wakilci jam’iyyu 33 da suka yi rijista da Hukumar INEC ne a Jihar Filato.
Aminiya ta gano mazavar Qua’an Pan ta Kudu ne take da mafiyawan mata ‘yan takara, inda mazabar take da ‘yan takara mata hudu.
‘Yan takarar sun hada da Anna Lagya, a jam’iyyar ABP da Maryam Baba a DA da Zainab Dogo a PDP da kuma Hassana Salihu Kwande a jam’iyyar SDP.
Mazabar Lantang ta Arewa ta (II) tana ke biye da mazabar Qua’an Pan ta Kudu, inda take da ‘yan takara mata uku. ‘Yan takarar sun hada da Mariam Ada Bala (ADC) da Alice James Wayi (ANN) da kuma Nancher Patricia Wapjin a jam’iyyar MPN.
Mazabar Shendam da Riyom da Jos ta Gabas da Mangu ta Arewa da kuma Langtang ta Kudu (Mabudi) suna da mata bibbiyu da za su yi takara.
Haka ma mazabar Kanam ta (I) da Pankshin ta Arewa da Jos ta Gabas suna da ‘yan takara mata bibbiyu.
Mazabun da suke da ‘yan takara mata daya sun hada da Barkin Ladi da Pengana Bassa ta (I) da Rukuba Irigwe da kuma mazabar Bokkos.
Sauran mazabun da suke da ‘yan takara mata daya sun hada da Jos ta Arewa maso Yamma da Kanke da Langtang ta Arewa ta (I) da kuma Mangu ta Kudu.
Mazabun da ba su da ‘yan takara mata sun hada da Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Mikang da Qua’an Pan ta Arewa da Kanam ta (II) da kuma Wase.
Aminiya ta gano takardar da nuna babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta tsayar da ‘yan takara mata biyu da suka hada da Zainaba Dogo a Qua’an Pan ta Kudu da kuma Dusu Esther a mazabar Jos ta Arewa maso Yamma, inda kuma jam’iyya mai ci APC a Jihar Filato ba ta tsayar da ‘yar takarar majalisar dokoki mace ba.
Jihar Filato dai tana da ‘yan majalisa 24 ne.

ADVERTISEMENT