✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata a nemi ilimi kuma a koyi sana’a – Binta Abdullahi Kowa

Sunan Hajiya Binta Abdullahi Kowa ko Mamawo Kowa sananne ne a wajen mata da matasa masu harkokin kasuwanci a birnin Kaduna. Ita ce Babbar Jami’ar…

Sunan Hajiya Binta Abdullahi Kowa ko Mamawo Kowa sananne ne a wajen mata da matasa masu harkokin kasuwanci a birnin Kaduna. Ita ce Babbar Jami’ar Gudanarwar Kamfanin Kowa Group of Companies da ke Kaduna, ta kuma yi suna wajen taimakon mata da yara marasa galihu don dogaro da kansu. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana yadda ta taso da gwagwarmayar da ta sha da nasarori da kalubalen da ta fuskanta a rayuwa:

 

Tarihina:

Sunana Hajiya Binta Abdullahi Kowa, an fi sanina da Hajiya Mamawo Kowa. An haife ni a garin Samarun Zariya a 1980. Mahaifina sanannen dan kasuwa ne wato marigayi Alhaji Abdullahi Kowa Store Samaru. Na yi firamare a Therbow da ke GRA, Zariya, na yi sakandare a Demonstration School da ke Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Daga nan na shiga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya inda na karanta Kimiyyar Dakin Karatu da Bayanai. Na yi aure ina da ’ya’ya uku namiji daya mata biyu.

Ni ce Manajar Darakta kuma Babbar Jami’ar Gudanarwar Kamfanin Kowa Global Concept Limited, kuma ina da gidauniya da muka assasa domin taimaka wa marasa karfi wajen daukarsu aiki da koya musu sana’o’in da za su dogara da kansu.

Ayyukana:

Duk da cewa na yi karatu har matakin digiri kuma na kammala ina da karancin shekaru, amma ban yi sha’awar neman aikin gwamnati ko kamfani ba, kuma na kammala makarantar ce a gidan mijina domin mahaifinmu mutum ne mai son ’ya’yansa mata su zauna gidajen mazansu. Amma da Allah Ya kaddara rabuwata da mijina sai na dawo gida domin babban burina shi ne in ga na kafa al’umma sun dogara da kansu. Sai na ga dole sai na fara sana’a da kafa kananan masana’antu don inganta rayuwar matasa da mata. Wannan shi ne burina kuma ina da sha’awar shiga cikin masu son ci gaban matasa da mata amma dukkansu ba zai yiwu ba sai na hada da siyasa.

A yanzu haka muna da gidauniya da muke kokarin kafawa da za ta rika tallafa wa al’umma musamman mata da wayar wa matasa kai wajen hana su harkar daba da shaye-shaye da suke addabar al’ummarmu musamman a nan Arewa. A yanzu haka mun yi nisa wajen kafa gidauniyar har mun fitar da shugabannin riko, inda nake shugabar riko.

Sunanta Gidauniyar Global Concert Initiatibes in Northern Nigeria. Mun assasa ta ce don kare hakkin yara da mata da koya musu sana’a da tallafa musu don dogaro da kansu a duk halin da suka tsinci kansu a rayuwa. Kuma muna ilimantar da su zamantakewar rayuwar gidan aure da sulhu tsakaninsu da mazan aurensu.

 

Yadda na fara kasuwanci:

Na fara kasuwanci ne bayan rabuwa da maigidana. Kasancewar mahaifina na da  rukunin shaguna wato Plaza, sai na karbi shago daya na fara sayar da kayan sawa na mata, saboda shi ma da kadan ya fara, wanda hakan ya sa ake masa lakabi da KOWA STORE. Daga nan sai Allah Ya albarkaci lamarin, inda harkokkin kasuwancin nawa suka rika bunkasa. Wannan ya sa sai na bude kamfani wanda na sa ma suna Kowa Global Concept Limited. Da kamfanin har na fara karbar kananan kwangiloli har ya kai ana ba ni kwangila a jami’a. Yanzu cikin ikon Allah ina samun manyan ayyuka sosai, kuma ina yi.

 

Abubuwan da na koya wajen iyayena:

Na koyi abubuwa da dama wajen mahaifina, Allah Ya kyautata makwancinsa, amin. Musamman wajen taimakon al’umma da ginawa ko gyara masallatai da daukar nauyin marayu su zama ’ya’yansa domin yana da arziki. Idan mabukata sun zo wajensa za ka ga yadda yake ba mu kudi mu ba su, wannan ya sa muka koya kuma muka saba da hakan. Haka lokacin azumi, mun koyi kyautata wa mutane. Sannan mutum ne mai zumuncin gaske. Ita ma mahaifiyata ta kasance mai yawan hakuri da ibada da son mutane. Mun koyi halayen kirki sosai a wajenta. Mun samu tarbiyya sosai wajen iyayenmu ni da sauran ’yan uwana.

 

Nasarori:

Alhamdulillah. Dole zan fara da yi wa Allah godiya musamman ganin yaddda Ya kawo ni wannan lokaci cikin koshin lafiya. Tabbas wannan kadai wata ni’ima ce wadda dole mu yi wa Allah godiya a kanta. Sai kuma inda Allah Ya taimake ni burina suna ta cika kamar yadda na roke shi. Cikin taimakon Allah yanzu ina da kamfanina da ma’aikatana kuma duk ina kokarin ganin na kyautata musu yadda ya dace, dukkanmu muna zaman amana tare da juna. Wannan babban nasara ce a gare ni. Ina godiya ga Allah.

Sannan gidauniyar da na yi magana a baya, dama can na fara ayyukan taimako kamar yadda na ce na gada mahaifina. Kawai na yi tunanin samun gidauniyar ce domin kara samun karfin gwiwa da fadada lamarin. Don taimakon al’umma su yi farin ciki ba karamin nasara ba ce a wajena, kuma ina matukar alfahari da haka.

 

Kalubale

Kamar yadda na fada a baya, kowane dan Adam yana da kaddarar da Allah Ya dora a kansa, wannan haka yake. Da farko dai na fuskanci kalubale wajen zamantakewar rayuwa da kuma rashin gaskiyar wadansu mutane da dama da na yarda da su. Sannan kuma wadansu mutanen masu aiki a karkashinka idan ba ka yi dace ba, da su za a rika bibbiya tare da lalata lamuranka. Amma duk da haka, na lura dcewa mutumin da za ka yi hulda da shi sai ka sa natsuwa da hankali da lura kuma sai ka sa hakuri da kawaici, idan ka yi haka da yardar Allah ba za ka samu matsala ba, ko ka yi da-na-sani.

 

Abin da nake so a tuna ni da shi

Babban abin da nake so a rika tuna ni da shi, shi ne ni a ce ni mace ce a cikin mata wadanda take da buri kuma take matukar son ganin ta inganta rayuwar mata ’yan uwanta da matasa.

 

Babban burina a rayuwa?

Babban burina bayan habaka harkokin kasuwancina shi ne in zama mai taimako tare da gina al’umma kuma in inganta rayuwar mata da zawarawa a duk fadin Arewa.

 

Wanda nake koyi da shi

Kai-tsaye ina kokarin koyi ne da kyawawan halayen mahaifina, domin an shaide shi da cewa mutum ne mai yawan raha da zumunci da son ci gaban al’umma. Sai kuma koyi da mahaifiyata wajen hakuri da iya zamantakewar rayuwa musamman wajen zamanta da abokan zama da danginta. Ba ni da wani abin koyi da ya wuce su.

 

Shawarata ga mata

Masha Allah. Tabbas matsalolin mata sai mata, wani abin ba zai fadu a nan ba. Amma zan jawo hankalinsu su yi kokarin samun ingantaccen ilimin addini da na zamani kuma su rike sana’a domin su yi dogaro da kansu kuma su taimaki iyalansu.

Sannan ina kira ga jama’a baki daya cewa in mutum ne yau, gobe ba shi ba ne. Don haka mu daina hassada da nuna wa juna bakin ciki. Mu rike gaskiya da amana, kuma mu ji tsoron Allah cikin dukkan lamuranmu na yau da gobe. Idan muka rike wadannan abubuwan tabbas rayuwarmu za ta yi kyau.

 

Abincin da na fi so

Shinkafa da hadin ganye (salad) da kuma dambun nama, sai tuwon masara da miyar ganye.

 

Tufafin da na fi so

Na fi son manyan riguna domin suna ba ni damar  walwala kasancewar yanzu na fara yin jiki ba kamar da can ba. Ina son atamfa da leshi amma shadda ba ta dame ni ba.