Search
Subscribe
Mata a rika biyayya a zaman aure  –  Iyar Garin Kano

Hajiya Umma Aminu Sanusi Iyar Garin Kano

Mata a rika biyayya a zaman aure  –  Iyar Garin Kano

Hajiya Umma Aminu Sanusi ita ce Iyar Garin Kano, wato sabuwar sarautar da Sarkin Kano Malam Muhamamdu Sanusi II ya kirkiro ya nada yarsa  a daidai lokacin da aka yi bikin rantsar da shi a matsayin Sarkin  Kano. Aminiya ta tattauna da ita game da irin fadi-tashin da ta yi a rayuwarta da ayyukan da ta shafe shekara 35 tana yi Gwamnatin Jihar Kano da Gwamnatin Tarayya da irin nauyin da ke kanta a matsayinta na Iyar Garin Kano. Ga yadda hirar ta kasance:

Tarihina

Sunana Hajiya Umma Aminu Sunusi. Mahaifina shi ne marigayi Ciroman Kano Ambasada Aminu Sanusi. An haife ni a 1957. Kamar yadda al’adar mutanen da take musamman kuma gidan sarauta dan fari ba ya girma a gaban iyayensa, sai dai kakanni, don haka ni ma na taso a hannun kakana Sarkin Kano Malam Sanusi. A wurinsa na zauna har zuwa lokacin da ya yi murabus ya koma Azare. Kasancewar muna makaranta a wancan lokacin sai aka bar mu a nan Kano.

Na yi karatun firamare a Makarantar Cikin Gida ta Kofar Kudu. Daga nan sai na koma Makarantar ’Yan mata ta Shekara, bayan na kammala sai na shiga Kwalejin ’Yan mata (GGC) ta Dala. Daga nan sai na tafi Kwalejin Share-Fagen Shiga Jami’a ta Zariya. Daga nan na samu shiga Jami’ar Bayero inda na karanci Harkokin Mulki (Public Administration). Bayan na kammala sai na yi aikin yi wa kasa hidima a Ma’aikatar Walwalar Jama’a.

Aiki

Na fara aiki a Ma’aikatar Daukar Ma’aikata ta Jihar Kano. Muna nan sai aka ba maigidana  Kwamishina a Jihar Neja da yake dan can ne. Da muka koma Neja sai na ci gaba da aikina a can. To Bayan an yi juyin mulki lokacin Janar Buhari sai muka dawo Kano  sai maigidana ya ci gaba da aikinsa na koyarwa a Jami’ar Bayero, ni kuma na koma aiki a Jihar Kano. Ina nan ina aiki har na kai matsayin Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Mata.

Daga nan sai aka kira ni na je kwas a Cibiyar Nazarin Harkokin Mulki da Bukatun Kasa (NIPPS) da ke Kuru a Jos. Bayan na dawo na ci gaba da aikina inda na zauna a ma’aikatu daban-daban. Ina nan ina aiki sai na nemi canjin aiki zuwa Gwamnatin Tarayya. A can ma Abuja na zauna a ma’aikatu daban-daban har zuwa lokacin da na yi ritaya a watan Disamban bara.

Nasarori da kalubale

A rayuwa dole ne wata rana mutum ya sha zuma wata rana kuma ya sha madaci. Amma idan mutum ya yi imani da Allah ya san komai mai zuwa ne ya wuce. Batun nasara kuwa alhamdulillahi domin ina yi wa Allah godiya bisa abubuwan da Ya yi min. Ba na mancewa a lokacin da muka dawo Kano daga Neja a lokacin mulkin Gwamnan Kano Iya Kwamanda Hamza Abdullahi ba a daukar mace a matsayin shugaba, amma bayan ya duba takarduna da ayyukan da na yi sai Gwamnan ya amince aka dauke ni. Na gode wa Allah da Ya sa na yi aiki ba tare da ba Gwamnan kunya ba. Ga shi yanzu ta sanadina ana ci gaba da daukar mata a wannan aiki. Haka kuma ina daga cikin mata na farko da suka samu mukamin Babbar Sakatariya. Har ila yau ni ce mace ta farko daga Jihar Kano da ta fara zuwa karatu Cibiyar NIPPS da ke Kuru. Sannann kuma ga sarautar da aka yi min ta Iyar Gari. Alhamdulillahi babu abin da zance sai godiya.

Iyali

Maigidana shi ne marigayi Farfesa Musa Abdullahi wanda ya rike mukamin Shugaban Jami’a. ’Ya’yanmu bakwai tare da shi.

Sarautar Iyar Gari

Wannan sarauta sabuwar sarauta ce wacce Mai martaba Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II wanda kanena ne ya ba ni ita. Duk da cewa a tsarin sarautar Sullubawa da wuya ka samu an nada mace sarauta, sai dai cewa a koyaushe zamani yana zuwa da canji. Wannan ba shi ne karo na farko da aka ba mace sarauta a wannan masarauta ba, domin marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya yi wa babbar ’yarsa sarautar Magajiyar ’Yan Sarki. Haka kuma wannan Sarkin lokacin yana Dan Maje ya yi wa uwargidansa sarautar Giwar Dan Maje.

Ana nan ana shirye-shiryen bude mana ofis inda za mu rika gudanar da harkokin wannan sarauta. Kasancewar Sarki mai son ci gaban talakawa ne, musamman ta fuskar ilimi da tattalin arziki, don haka za mu taimaka masa wajen cika wannan buri nasa.

A aikace-aikacen da za mu yi za mu rika taimaka wa mata wajen ilimintar da su tare da sama musu sana’o’i.  Haka kuma duk lokacin da wani abu ya bullo za mu yi kokarin wayar wa mata kai. Duk da cewa gwamnati tana iya nata kokarin a kai, mu ma a bangaren masarauta muna ganin ya dace mu bada tamu gudummawar wajen ci gaban al’umma.

Za mu yi wadannan ayyuka ne tare da hadin kan kungiyoyi. Ba wai kawai mata za mu koya wa sana’o’i ba har da matasa wadanda ke da sha’awar yin sana’o’i amma ba su da hali, za mu koya musu sana’ar da suke so tare da ba su wani tallafi don dogaro da kai.

Za mu nemi tallafi daga jama’ a wadanda koyaushe a shirye suke su sa dukiyarsu a abubuwan alheri irin wannan. Za mu neme

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin