✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata ku rika shiga harkokin siyasa ana damawa da ku – A’ishatu Mbaka

Tarihin rayuwarta: Sunana A’ishatu Mbaka. An haife ni a Unguwar Kawo a cikin  Jihar Kaduna a shekarar 1959. Na yi karatun firamare a L.E.A Kawo…

Tarihin rayuwarta:

Sunana A’ishatu Mbaka. An haife ni a Unguwar Kawo a cikin  Jihar Kaduna a shekarar 1959. Na yi karatun firamare a L.E.A Kawo amma na ci gaba a G.S.S. Zonkuwa duk a Jihar Kaduna. Daga nan na cigaba da karatu a Kwalejin Horar da Malamai  (K.T.C.) a Kaduna inda na kammala a shekarar 1977. Na kuma yi makarantar Ungo-zoma a Tudun-Wada ita ma a jihar Kaduna daga 1982 zuwa 1984. Dag anan sai na ci gaba a Kwalejin Kimiya da Fasa’a ta Gwamnatin Tarayya da ke Jihar Nasarawa.  Bayan na kammala na samu babbar difloma dina na kuma yi karatun digiri a Jami’ar gwamnati da ke garin Keffi ta Jihar Nasarawa inda na kammala a shekarar 2004.  Sannan na yi wasu kwasa-kwasai da dama a ciki da wajen Jihar Nasarawa.

Ayyuka:

Bayan na kammala karatu sai na shiga harkokin kasuwanci na wasu lokuta kafin daga bisani na shiga harkar siyasa inda har na rike mukamin Shugabar Jam’iyyar Labour a Jihar Nasarawa. Idan za a iya tunawa na fito takarar gwamnan jihar nan a inuwar Jam’iyyar Labour a zaben gwamnoni da aka gudanar a shekarar 2015. Kodayake kafin zaben, gwamnan jihar nan mai ci, Umaru Tanko Almakura ya roke ni in janye masa, na amince da bukatarsa na sauka na hakura na kuma ba shi goyon baya wanda hakan ya sa da ya yi nasara bai yi wata-wata ba ya ba ni mukamin Babbar mai taimaka masa ta musamman. Wadannan su ne kadan daga cikin ayyuka da mkkaman da na rike kawo yanzu amma yawancinsu na siyasa ne don ni ‘yar siyasa ce.

kungiyoyi:

Ina cikin kungiyoyi da dama a ciki da wajen jihar nan wadanda suka hada da kungiyar Co-operatibe da wata kungiya da akafi sani da ANMFI a takaice wacce Babban Bankin Najeriya (CBN) ta kafa don taimakawa mata wajen samun basussuka musamman na kudi. Ni ce mukaddashin Shugabar kungiyar ta kasa. Ina kuma cikin wata kungiya wacce ake kira NUCOWA a turance da kungiyar JIB da kungiyoyin mata da na addini daban- -daban a ciki da wajen jihar nan da lokaci ba zai bari in bayyana su duka ba.

Nasarorin da na cimma a rayuwata:

A gaskiya da ikon Allah zan ce na samu nasarori da dama a rayuwata kawo yanzu. Kuma zan ce manyan nasarori da na samu su ne na damar da nake samu na shugabannci ko in ce jagorar al’ummata. Kamar yadda na bayyana maka a baya kuma kamar yadda ka sani a yanzu ina rike da mukamin Mai Taimakawa gwamnan jihar nan na musamman. Kafin wannan mukami na kasance shugabar jam’iyyar Labour a jihar nan. Na kuma rike shugabancin kungiyoyi da dama a ciki da wajen jihar nan. Saboda haka ina ganin wadannan da sauran da ban bayyana ba a matsayin nasarori da na samu a rayuwata. Don ta wadannan hanyoyin ne nake ba da tawa gudumawa wajen inganta rayuwar al’ummata a jihar nan da kasa baki daya. Allah Ya albarkace ni da ‘ya’ya 6 watau maza 3 mata 3 tare da maigidana marigayi da aka fi sani da Manjo Mbaka. Allah Ya jikansa. Ya rasu ne a sanadiyyar hadarin jirgin sama da ya hallaka wasu manyan sojojin kasar nan a shekarar 1992 wadanda ke tafiya Jaji da ke Jihar Kaduna. Yana cikin wadanda suka rasa rayukansu a jirgin don Manjo ne kafin mutuwarsa. Saboda haka ina ganin wadannan a matsayin wasu daga cikin nasarorin da na cimma a rayuwata kawo yanzu kamar yadda na bayyana a baya.

Abin da zan so a tuna da ni:

Ni dai a gaskiya zan so a tuna da ni a bangaren siyasa ne. Don ka ga ba yabon kai ba kamar yadda ka sani ni ce mace ‘yar siyasa ta farko da ta fito takarar kujerar gwamnan jihar nan kuma ba waina sha kaye ba ne gwamna ne ya bukace ni in hakura masa ni kuma na ga mutuncinsa da kyawawan akidojinsa na hakure masa. Saboda haka ina so al’umma baki daya musamman mata ‘yan uwana ba wai kawai su tuna da ni ba su kuma yi koyi da yadda nake fafatawa a harkar siyasa. Watau ya kasance idan ana maganar mata da aka dama da su dumu-dumu a harkar siyasa a jihar nan da ma kasa baki daya a ambaci sunana. Ina nufin idan ana maganar mata ‘yan siyasa da suka kawo canji mai ma’ana a rayuwan al’ummansu musamman mata ta hanyar siyasa yakasance sunana ma yana cikin jerin sunayen wadannan mata. A takaice dai ka ji abin da zan so a tuna da ni kenan bayan na bar duniyar nan.

Shawarata ga mata ‘yan uwana:

Shawara da nake bai wa mata ‘yan uwana a kullum ita ce su rika shiga harkokin siyasa ana damawa da su. Don kamar yadda ka sani bincike ya nuna cewa a duk inda aka samu mace tana shugabanci ana samun gagarumin ci gaba da nasarori da dama. 

Kuma lokaci ya wuce da mace za ta rika dogaro da mijinta. Yakamata ta tashi ta kama sana’a idan ba ta samu damar karatu ba don amfanin kanta da ‘ya’yanta da al’umma baki daya. Ina kuma nanata cewa mata a shiga siyasa don a gaskiya har yanzu an bar galibin matan kasar nan a baya a harkar siyasa don sun kasa fahimtar muhimmancin shiga harkar ana damawa da su. Ka ga a yau wadannan nasarori da na cimma a rayuwa da na bayyana maka zan ce duk na samesu ne ta harkar siyasa. Ka ji takaitaccen shawara da nake da shi ga mata ‘yan uwana.  Nagode.