✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata ku shiga siyasa a dama da ku – Khadijat Abdullahi Adamu

Barista Khadijat Abdullahi Adamu matar tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu ce, Lauya ce kuma ’yar siyasa. A yanzu ita ce Manajan otel din…

Barista Khadijat Abdullahi Adamu matar tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu ce, Lauya ce kuma ’yar siyasa. A yanzu ita ce Manajan otel din Keffi Hotel da ke garin Keffi hedikwatar Karamar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa. A zantawarta da wakilinmu ta bayyana tarihin rayuwanrta inda ta bukaci ’yan uwanta mata su shiga harkar siyasa a dama da su.Ta kuma shawarci gwamnatoti a dukkan matakai su rika aiwatar da hukuncin kisa ga duk wanda ya aikata laifin fyade ga ’ya mace da sauransu:

Tarihin rayuwana:

Sunana Barista Khadijat Abdullahi Adamu. An haife ni a 1970 a garin Potiskum da ke Jihar Yobe a yau. Na yi  firamare a Potiskum a makarantar firamare ta Kara Primary School daga 1976 zuwa 1981. Daga nan na yi makaranta sakandare a Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta Gwamnati (GGSS) ta Potiskum daga 1981 zuwa 1986. Da na kammala sakandaren ina ’yar shekara 16 duk da ina da karancin shekaru a shekarar na wuce Jami’ar Maiduguri wato daga 1986 zuwa 1988 inda na yi karatun diploma a fannin shari’a. Daga nan na ci gaba da karatun digiri dina a jami’ar daga 1988 na kammala a 1992. Daga nan na tafi Makarantar Lauyoyi ta Najeriya (Nigerian Law School) a Legas inda na kammala a 1993. Allah Ya taimaka na ci jarrabawata a zama na farko. Don a lokacin akan ba da dama mutum ya sake rubuta jarrabawa har sau biyar idan bai yi nasara ba. Amma ni a zama na farko Allah Ya taimaka na ci jarrabawar inda bayan na kammala sai na tafi hidimar kasa a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Filato a 1994. Na yi aure a 1993 wato kafin in je hidimar kasa ke nan. Daga nan na zo na  zauna a gida na wasu lokuta kafin daga bisani in yi wasu ayyuka daban-daban da shiga kungiyoyin aiki namu na mata da dama da lokaci ba zai ba ni damar bayyana su duka ba.

 

Abubuwan da na koya wurin iyayena

A gaskiya iyayena sun koya mini kyawawan dabi’u. Ba ni kadai ba har da sauran ’yan uwana duk mun samu tarbiyya tagari wurin iyayenmu, musamman a fannin neman ilimi na zamani da na addini. A gaskiya ba zan taba mantawa ba yadda iyayenmu suka rika karfafa mu a wannan fanni. Sun kuma koya mana girmama na gaba da mu da magabata da sauran al’umma baki daya. Kuma a gaskiya a rayuwarmu yanzu muna cin moriyar wadannan kyawawan dabi’u da muka koya a wurinsu. Kuma mu ma abin da kullum da yardar Allah muke koya wa namu ’ya’yan ke nan don ya amfane su gobe. Saboda haka, a takaice muna cin moriyar kyakkyawar tarbiyyar da iyayenmu suka koya mana lokacin da muke tasowa.

 

Kalubale da nake fuskanta

A gaskiya a yanzu kalubale da nake fuskanta bai wuce na jama’a ba. Kamar yadda ka sani maigidana sanannen dan siyasa ne da ya yi Gwamnan Jihar Nasarawa kuma a yanzu Sanata ne karo na biyu. Saboda haka a kullum muna tare ne da jama’a inda a kullum muke iya kokarinmu mu ga mun tallafa musu a fannoni da dama. Koda yake ba na kallon haka a matsayin kalubale. Don na tabbata haka shugabanci ya gada. Idan Allah Ya aza maka nauyin al’umma ya kamata ka taimaka musu. Amma ba za ka iya yi wa kowa yadda yake so ba, amma dole ka yi iya kokarinka. Saboda haka ina godiya ga Allah da Ya ba ni wannan dama tun tasowata har zuwa wannan matsayi da nake yanzu kuma ba abin da zan ce sai alhammdulillah.

 

Nasarori da na cimma a rayuwa

To, kamar yadda na bayyana maka a baya na gode Allah da Ya ba ni wannan dama a rayuwata. Kuma kamar yadda aka sani da yardar Allah na shiga tarihi cewa ni ce  Uwargidan Gwamnan Jihar Nasarawa ta farko a zamanin farar hula. Kuma idan za ka iya tunawa lokacin da nake rike da wannan mukami na kirkiro tare da aiwatar da wasu muhimman shirye-shirye da suka taimaka matuka wajen kawo canji mai ma’ana ga rayuwar al’ummar jihar nan baki daya musamman mata ’yan uwana da kasa baki daya. Kuma har yanzu muna tare da jama’a muna tallafa musu iya gwargwado. Kuma jama’a da dama daga ciki da wajen jihar nan suna yaba mana a kullum. Za ka iya tabbatar da haka ta wadannan lambobin yabo da kake gani a nan ofishina. Duk daga kungiyoyi da al’ummomi daban-daban nake samu a kusan kullum inda suke yaba wa ayyukan tausayi da muke yi musu da yardar Allah. Saboda haka ba yabon kai ko wani abu makamancinsa ba, zan iya cewa kawo yanzu a rayuwata na samu dimbin nasarori. Don na tabbata ita nasara a rayuwa ba ta fannin tara abin duniya ba ce. Amma a kan kwatanta nasarar shugaba ta fannin irin ayyukan agaji da yake yi wa al’ummarsa.

 

Abin da ya ba ni sha’awar shiga siyasa

Na shiga harkar siyasa ba kawai don na auri kwararren dan siyasa ba ne. Na shiga harkar ce don in ba da gudunmawata wajen tallafa wa al’ummata. Na lura ita siyasa wata hanya ce ta tallafa wa al’umma a fannin rayuwa. Kuma tunda na fara kawo yanzu, abin da nake yi ke nan kamar yadda na bayyana a baya. Saboda haka a takaice zan ce na shiga harkar ce don in ba da gudunmawa daidai gwargwado ga ci gaban al’ummata kamar yadda na bayyana ba don kawai maigidana dan siyasa ba ne.

 

Shawarata ga ’yan uwana mata

Ina kira na musamman ga ’yan uwana mata a jihar nan tamu ta Nasarawa da kasa baki daya cewa, lokaci ya yi da za su shiga harkar siyasa ana damawa da su dumu-dumu. Idan aka lura a nan Jihar Nasarawa da kasa baki daya an yi zaben bana an gama kuma alhamdulillah jam’iyyarmu ta APC ce ta lashe kusan dukan zabbubukan tun daga Gwamnatin Tarayya zuwa jihohi. Idan ka lura duk da yake mata sun fito takarar wasu kujerun siyasa, amma a gaskiya ba su fito da yawa yadda ake so ba. Kuma wani abin takaici shi ne yadda galibin wadannan mata da suka fito takarar ba su yi nasara ba. Kuma ina sanar maka cewa hakan ya faru ne saboda irin takurawa da maza ke yi wa mata. An hada baki ne aka kada mata a zabbubukan bana.

Kuma a gaskiya hakan bai dace ba don idan aka bai wa mace damar shugabanci za ta iya taka rawar gani sabanin yadda galibin maza ke tunani. Kuma ina kira ga sauran mata ’yan uwana cewa duk lokacin da ’yar uwarsu mace ta fito takarar kowace kujera to su bar maganar kyashi da gaba su mara mata baya don nasararta tamkar nasararsu ce baki daya, don ita ta fi sanin damuwarsu fiye da takwarorinmu maza.

A fannin jefa kuri’a kuma ina so in tunatar da gwamnatoci a dukkan matakai kada su manta cewa a bana mata sun taka muhimmiyar rawa wajen kada kuri’a inda kusan kashi 80 cikin 100 na kuri’un da aka jefa a zaben bana a jihar nan da kasa baki daya nasu ne. Saboda haka ya zame wa gwamnatocin dole su yi tafiya da su a shirye-shiryensu musamman ta fannin kula da kiwon lafiyarmu da iliminmu da tsaronmu da sauransu. Kuma a karshe ina so in yi kira na musamman ga gwamnatoci a dukkan matakai su sa wani hukuncin mai zafi kan cin zarafin mata musamman ma fyade da sauransu. Idan mutum ya yi wa mace fyade hukuncin kisa kai-tsaye ya kamata a yi masa.

Domin duk macen da aka yi mata fyade an bar ta da wannan tabo ke nan har iya rayuwarta. Kuma idan Allah bai kiyaye ba har kashe kanta za ta iya yi saboda takaicin wannan mummunar ta’asa da aka yi mata.