Search
Subscribe
Mata mu daina yarda ana barinmu a baya a harkar siyasa – Stella I. Oboshi

Misis Stella I. Oboshi

Mata mu daina yarda ana barinmu a baya a harkar siyasa – Stella I. Oboshi

Misis Stella I. Oboshi gogaggiyar ’yar siyasa ce da ta fara siyasa tun tana  budurwa. Ta rike mukaman siyasa daban-daban a Jihar Nasarawa. A yanzu haka ita ce shugabar mata ta Jam’iyyar PDP a Jihar. A tattaunawarta da wakilinmu ta bayyana tarihin rayuwarta da yadda ta fara siyasa da sauransu. Ta kuma shawarci mata su rika fitowa neman kujerun siyasa maimakon su jira sai an nada su mukamai.

 

Tarihin rayuwata:

Sunana Honorabul Stella Oboshi. An haife ni a 1975. Ni ’yar kabilar Alago ce daga Karamar Hukumar Doma a Jihar Nasarawa. Na yi karatun firamare a RCM Primary School da ke garin Doma. Daga nan na ci gaba a Kwalejin Kimiya ta Gwamnati da ke Doma wanda yanzu aka mayar da ita  Kwalejin Gwamnati. Bayan na kammala a 1984 na ci gaba da karatu a Kwalejin Kimiya da Kere-Kere ta Jihar Filato da ke garin Jos inda na yi karatun Diploma a Fannin Kudi (Accounting). Daga nan na koma Jihar Nasarawa inda na ci gaba da karatu a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya da ke garin Nasarawa hedikwatar Kamarar Hukumar Nasarawa inda na samu Babbar Diploma a Fannin Kudi. Bayan wannan ban samu damar tafiya hidimar kasa ba, saboda a lokacin shekaruna sun wuce na tafiya hidimar kasa. Shi ya sa aka ba ni shaidar shekaruna sun wuce yin hidimar kasa (NYSC) wadda ke nuna cewa lallai na kammala karatuna da kuma hujjojin da suka hana ni tafiya hidimar kasar. A yanzu ina da aure da kuma da ’ya’ya. Wannan shi ne kadan daga cikin tarihin rayuwata.

Tarbiyyar da na koya wurin iyayena:

Ban yi girma a hannun iyayena ba. Tun ina karama iyayena suka tura ni goyo a wurin wacce mahaifiyata ke biye da ita wato yarta. A wajenta na girma na koyi tarbiyya mai kyau. Na ce tarbiyya mai kyau don kamar yadda ka sani idan yaro ya tashi a gidan wadansu daban wadanda ba iyayensa ba yakan zama horarren yaro don ba zai samu dama ya rika yin abin da ya ga dama ba, musamman wadanda ba su dace da shi ba. Don wadansu yaran da suka girma a wajen iyayensu za ka tarar iyayensu suna shagwaba su hakan a karshe ya sa su kasance marasa kyakkyawar tarbiyya.

Na yi karatuna a wurin Yayar mahaifiyata inda na rika yin karatu kuma ina taya ta aiki a gona. Idan na dawo daga makaranta kuma wasu lokutan nakan taimaka mata a kasuwancin da take yi a lokacin na sayar da giyar gargajiyar nan da ake kira burkutu. Idan ta dama giyar mukan kai kasuwa mu sayar. Kuma da haka ta yi ta tallafa mini har na kammala karatuna. Kuma a gaskiya ba zan taba manta wannan zama da na yi da ita ba, don ta koya mini tarbiyya mai kyau wadda nake cin moriyarta a rayuwata. Kuma a yanzu ba ni da abin da zan ce mata da ya wuce Allah Ya saka mata da alheri.

Yadda na shiga harkar siyasa:

Wato ba yabon kai ba idan ka binciki tarihin siyasata za ka gano tun ina budurwa na shiga harkar siyasa. Don a lokacin a garinmu duk lokaci da wata kungiya ko al’umma za su yi taro ko wani sha’ani na musamman da ya danganci siyasa, sukan gayyace ni in zo in zama sakatariya inda nake rubuta abubuwan da suke gudana a wajen tarurrukan. Haka aka rika gayyatata ire-iren zaman siyasar har na yi suna a yankinmu a kan wannan aiki da nake yi. A duk lokacin da za a yi taron siyasar babu wanda ke ja da ni a wannan matsayi na sakatariya kuma ba ni nake nema ba ’yan siyasar ne ke nemana in yi musu aikin wai don ina da baiwa na kuma kware a fannin. Harkar da na rika yi ke nan har zuwa shekarar 2004 inda na yanke shawarar fitowa takarar kujerar kansila a mazabata ta Galadimawa.

A zaben na kara ne da maza da suka kai 24 kuma a karshe na yi nasarar lashe zaben na kuma kasance mace ta farko da aka zaba a wannan matsayi a mazabarmu. Daga nan sai na sake neman mukamin Shugabar Karamar Hukumarmu ta Doma. Amma a karshe saboda danniya irin ta maza na samu mukamin Mataimakiyar Shugabar Karamar Hukumar. Kuma a tarihin kansilolin jihar mu muka fi dadewa a kujera inda muka yi shekaru 3 da rabi muna aiki wato a zamanin gwamnatin Abdullahi Adamu ke nan. Daga nan na ci gaba da harkokin siyasa har na sake fitowa takarar Shugabar Karamar Hukumar Doma a zaben shekarar 2015 da ya gabata a inuwar jam’iyyarmu ta PDP. Da ni da wadansu maza biyu muka tsaya takarar. Sai dai daga bisani shugabanni da masu ruwa -da-tsaki na jam’iyyarmu suka ba mu hakuri muka janye wa wani. Haka muka hakura muka janye masa kafin bayan zaben aka ce to mu da muka fito takarar muka kuma kashe kudi a lokacin kamfe da sauransu ya kamata a saka mana da alheri. Yadda aka yi aka ba ni mukamin Sakatariyar Karamar Hukumar ke nan.

Bayan wannan a zaben shugabannin jam’iyyarmu da aka gudanar kwanakin baya an sake ba ni mukamin Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP a TA Jihar Nasarawa  baki daya. Kuma kamar yadda ka sani mukamin da nake rike da shi ke nan har yanzu.

Matsaloli da nake fuskanta a wajen aiki:

Babban matsalar ita ce ka ga a yanzu gwamnati ba ta hannunmu kuma muna tare da jama’a. Kuma kamar yadda ka sani harkar siyasa ta fi tafiya da kyau ne idan akwai kudi a hannun ’yan siyasa. A yanzu muna ci gaba da rokon magoya bayanmu musamman mata don su

fahimci halin da muke ciki. Kuma muna yi musu alkawarin cewa da yardar Allah idan muka kwace gwamnati ta dawo hannunmu za mu tabbatar sun amfana da wadatattun abubuwan more rayuwa da sauransu kamar yadda muka saba a lokacin da muke da gwamnati. Saboda haka a takaice babbar matsalar ita ce ta rashin kudi. Matsala ta biyu kuma ita ce yadda wadansu maza ba sa barin matansu su shiga harkar siyasa musamman a jihar nan. Wadannan ire-iren maza sun dauka siyasa wata mummunar aba ce amma ba haka lamarin yake ba. Domin a wajena siyasa wata hanya ce ta bayar da gudunmawa wajen ci gaban kasa.

Saboda haka hana mata shiga siyasa da mazan ke yi ba karamin koma baya da kalubale ba ne a wajena musamman a kokarin da nake yi na jawo ra’ayinsu zuwa ga siyasa. Na karshe shi ne a yanzu ni kadai ce mace a tsakanin shugabannin jam’iyyarmu ta PDP a Jihar Nasarawa, sauran maza ne.  Duk da ba na samun sabani da su, amma zan so a ce mun kai akalla biyu ko uku a cikin tafiyar.

Nasarorin da na cimma a rayuwa:

To, kamar yadda na bayyana maka a baya ni dai a rayuwata na yi ta ce a bangren siyasa.  Tunda na kammala karatu ban taba yin wani aiki koda na gwamnati ne ba ban da siyasa. Saboda haka nasarorin da na cimma a fannin siyasa ne. Ka ga babbar nasarar ita ce tunda na shiga siyasa nake ta jan ra’ayin ’yan uwana mata suna tafiya da mu a Jam’iyyar PDP a jihar nan da kasa baki daya. Kuma suna ba mu cikakken hadin kai ina kuma samun yabo a kullum a wannan bangare. Sannan na samu nasarar yadda wata mace mai suna Misis Patricia Akwashiki ta fito takarar fitar da gwani a karkashin jami’iyyarmu ta PDP a Jihar Nasarawa, duk da yake ta fadi, amma ni na yi sanadiyyar da har ta fito takarar.  Ka ga wannan ma nasara ce a gare ni.

Shawarata ga mata:

A kullum shawarar ke nan su rika fitowa neman kujerun siyasa a ciki da wajen jihar nan. Ka ga lokaci ya wuce da mata za mu rika jira a nada mu kwamishinoni da daraktoci da sakatarori da sauransu. Mu ma ya kamata mu rika fitowa neman kujerun siyasa kamar takwarorinmu maza.

Kamar yadda na fada a baya ne,  ina mace na yi takarar kansila da maza 24 na yi nasara. Bayan wannan na yi takarar Shugabar Karamar Hukuma da ban samu ba sai aka saka mini da mukamin Sakatariyar Karamar Hukuma.  Kuma har yanzu ina kan neman kujerun siyasa a matakai daban-daban.  Don haka babu abin da maza za su yi, wanda mace ba za ta iya ba a bangaren siyasa. Na gawata an yi hira da ita a jaridar Aminiya tana fadin wai rashin kudi ne ke taka wa mata birki a harkar siyasa. Abin ya ba ni dariya, ai siyasa ba sai mai kudi ba.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin