Search
Subscribe
Mata su dage wajen neman ilimi – Hajiya Halima Diko

Hajiya Halima Diko

Mata su dage wajen neman ilimi – Hajiya Halima Diko

Hajiya Halima Diko ta fito ne daga Karamar Hukumar Birnin Kebbi a Jihar Kebbi. Tsohuwar malamar makaranta ce, wanda yanzu kuma Babbar Sakatariya ce a Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi  ta Jihar Kebbi. Mace ce mai son ci gaban jama’a musamman a bangaren samun ingantaccen ilimi. Aminiya ta tattauna da ita inda ta yi bayanin rayuwarta da gwagwarmayar da ta sha:

Tarihin rayuwata

Sunana Hajiya Halima Diko ni ’yar asalin Jihar Kebbi ce kuma an haife ni a garin Birnin Kebbi, na fara makarantar allo a makarantar Malam Na- Abu Liman a garin Birnin Kebbi, daga nan aka sa ni Santaral Firamare a 1977 na fara da rabin aji daga nan sai wata ’yar uwata da ke aure a garin Zuru ta dauke ni ta tafi da ni Zuru.

A Zuru na fara firamare a Makarantar Sami Gomo na shiga aji daya, da ma tun daga Birnin Kebbi na gama rabin aji, ina nan a Zuru na kai aji uku sai aka tafi da ni zuwa Legas na yi shekara biyu daga nan aka dawo da ni Birnin Kebbi inda na kare firamare a makarantar Makerar Gandu wadda ake kira Sakandaren Atiku Bagudu a yanzu a nan na yi aji shida zuwa bakwai.

Bayan na gama sai na ci jarrabawar zuwa Kwalejin ’Yan mata da ke Sakkwato (GGC) a 1982.

Bayan na gama sakandare sai na wuce zuwa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na yi karatun share-fagen shiga jami’a, na kuma ci gaba a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato bayan na shekara daya a Zariya, saboda a lokacin za a yi mini aure, a nan Jami’ar Usman Dan Fodiyo na yi digiri na farko. Bayan na gama sai na wuce yi wa kasa hidima inda aka tura ni Makarantar ’Yan mata ta Nana Girls da ke Sakkwato.

Bayan da na gama hidimar kasa, sai na samu aikin koyarwa inda aka tura ni Makarantar Sakandare ta Giginya da ke Sakkwato, ina nan ban shekara biyu ba a makarantar sai na samu aiki a Jami’ar Usman Dan Fodiyo aka tura ni ofishin Rajistara. Ina nan Sakkwato sai a 1991 aka kirkiro Jihar Kebbi sai na dawo gida na kama aiki a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Birnin Kebbi wato Waziri Umaru Federal Polytechnic.

A 1992 na koma aiki a karkashin jiha inda na fara aiki a Hukumar Fansho ta kananan hukumomi, daga nan sai aka canja ni zuwa Hukumar Fansho ta Malaman Firamare ni ce na bude wannan hukuma shekara ta goma a wannan hukuma.

Ina wannan hukuma har zuwa shekarar 2016, Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya nada ni a matsayin Babbar Sakatariya aka tura ni Ma’aikatar Mata ta Jihar Kebbi, bayan na yi ’yan watanni sai aka canja mini wurin aiki zuwa Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta Jihar Kebbi inda nake har yanzu. Yanzu shekarata biyu da rike wannan mukami na Babbar Sakatariya.

Kalubale:

Kalubale da zan ce na samu shi ne kamar aikin da na yi a Jami’ar Usman Dan Fodiyo, domin wuri ne na masu ilimi da tunani da sanin ya kamata, duk abin da mutum zai yi sai ya samu wani ya yi masa gyara, dole duk abin da za ka yi sai ka natsu duk wanda za ka yi hulda da shi malami ne ko dalibi sai ka kwantar da hankalinka. Kuma ka rika tunani wanda kake hulda da shi, domin mai zurfin ilimi da tunani ya san inda duniya ta nufa,

wanda duk ya yi aiki a irin wadannan wurare dole ya rika samun kalubale, amma kuma za ka goge a wajen aiki a ko’ina kana iya aiki.

Burina:

Burina shi ne in ga na gama aikin gwamnati lafiya, kuma idan mutuwa ta zo in cika da imani, domin babu wani buri ga ma’aikacin gwamnati illa ya kai matsayin Babban Sakatare ya kuma gama aiki gwamnati lafiya.

Tarbiyya daga iyaye:

A gaskiya iyayena sai dai in ci gaba da yi musu addu’ar Allah Ya saka musu da alheri, domin a kullum suna yi mini huduba da cewa duk inda nake in zama mai hakuri, kuma duk yadda na ga mutum in mutunta shi in ya girme ni in ba shi girman da Allah Ya ba shi. Sukan ce mini kada in zama mai wulakanta jama’a a duk irin mukamin da na samu. In rika daraja jama’a babba da karami. A kan haka ne duk ma’aikatar da na je za ka ga ina mu’amala da jama’a da zarar aka tada ni a wannan ma’aikata za ka ga jama’ar da muke aiki da su ransu na baci saboda zan tashi a wannan ma’aikata, ba komai ne ya jawo mini haka ba illa tarbiyyar iyaye da na dauka tun ina karama.

Kasashen da na je:

Na je Amurka da Saudiyya da Habasha da Tanzaniya da Nijar da Ghana.

Haduwa da maigida:

Maigidana aminin yayana ne ta nan ne muka hadu, domin yana zuwa wajensa, ta nan ne ya gan ni ya ce yana sona har Allah Ya hada mu muka yi aure. Yanzu muna da ’ya’ya shida maza uku mata uku suna nan da ransu.

Shawara ga mata:

Shawarata ga mata ita ce su dage wajen neman ilimin addini da na zamani musamman na addini don sai kin samu ilimin addini kafin ki san muhimmancin samun na zamani. Idan mace tana da ilimi ba shakka za ta taimaka wa maigidanta ta hanyoyi da dama.

Kuma ita kamar malama ce ga ’ya’yanta saboda haka dole ne ta nemi ilimi kafin ta iya koya wa ’ya’yanta tarbiyya. Iyaye mata su rika matsa wa mazansu wajen sanya ’ya’yansu a makaranta domin tarbiyyantar da su.

Haka su ma mata matasa wadanda ke makaranta su kauce wa ba malamai kudi ko kansu domin su ci jarrabawa, wannan ba karamar illa ba ce, in kin yi haka kin cuci kanki da iyayenki da kasa baki daya

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin