✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata sun fara fafata damben gargajiya a kasar nan

Wadansu ’yan mata sun fafata a wasan damben gargajiya, a wasan da ake ganin na maza ne zalla. Sashin Hausa na Gidan Rediyon BBC da…

Wadansu ’yan mata sun fafata a wasan damben gargajiya, a wasan da ake ganin na maza ne zalla. Sashin Hausa na Gidan Rediyon BBC da ya ruwaito labarin ya ce a farkon wannan makon an dambata a wasanni da dama a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke Marabar Nyanya a Jihar Nasarawa a kusa da Abuja, ciki har da damben mata. ’Yan matan da suka fafata masu suna Baby da Ramsy sun bukaci yin damben ne don kashin kansu, inda Baby ta wakilci Jihar Nasarawa, ita kuma Ramsy ta wakilci Kano.

Sun yi turmi biyu babu kisa kafin a raba su

 

Damben da aka yi kisa

  1. Kuronabairus daga Kudu ya buge Bahagon Gidewe
  2. Shagon Wale ya yi nasara a kan Shagon Ali Kanin Bello
  3. Karda Bakon Dole ya yi rashin nasara a hannun Bahagon Alin Ba-Ta-Isarka
  4. Shagon Tanko Guramada ya buge Dogon Inda daga Jamus
  5. Garkuwan Cindo Guramada ya doke Bahagon Sisco daga Kudu

Damben da ba kisa

  1. Shagon Aljanin Arewa da Kato Maikarfi daga Kudu
  2. Shagon Lawwali daga Arewa da Goloko daga Kudu
  3. Kuronabairus daga Kudu da Shagon Aljanin Arewa daga Arewa
  4. Tula daga Jamus da Shagon Kunnari Suda daga Kudu
  5. Dogon Na-Sigari daga Kudu da Shagon Goshin Jirgi daga Arewa