Da Dumi Dumi

Mata ta jefar da dan mijinta a kasuwa sai bayan shekara aka gano shi

Daga dama Malam Uba, mahaifin Gaddafi, sai Gaddafi da yayansa Faruk da kuma Isah Mai’unguwa
Daga dama Malam Uba, mahaifin Gaddafi, sai Gaddafi da yayansa Faruk da kuma Isah Mai’unguwa

Wani yaro mai suna Gaddafi mai kimanin shekara biyar da aka  ce ya bace kimanin shekara daya da rabi a Unguwar Hotoro Kano ya sadu da iyayensa.

A wancan lokaci matar mahaifinsa mai suna Maryam wacce take rikonsa ta ce yaron ya fita daga gida ne ba tare da an sani ba kuma ya bace inda aka neme shi aka rasa. Tun daga wancan lokacin ake ta cigiya kuma aka yi ta nema har aka gaji amma ba amo ba labari.

Mahaifin yaron, Malam Uba,  ya ce “Tun wajen karshen watan Disamban shekarar 2017, ina Abuja sai matata da ke Kano ta bugo mini waya cewa Gaddafi ya bace, yau kwana uku ba a gan shi ba. Kuma wai ba sa son su tayar mini da hankali ne ya sanya suka ci gaba da nema da ba da cigiya ba tare da sun sanar da ni ba har tsawon kwanakin saboda suna zaton ko za a same shi.”

Mahaifin ya ce wannan ya sanya shi tafi Kano, inda ya kai rahoto a ofisoshin ’yan sanda da na Hisba tare da bayar da sanarwa a gidajen rediyo da talabijin.

“Bayan mun yi cigiya da addu’a har kimanin wata shida ba amo ba labari, sai na fawwala wa Allah komai na hakura, na ci gaba da addu’a,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Malam Uba ya ce ya shiga tashin hankali da bakin ciki marar misaltuwa kan batan dansa, inda ta kai har wadansu suka rika zarginsa cewa ya hada baki da amaryarsa Maryam ce suka sayar da dan. Ya ce ya yi nadamar daukar ’ya’yansa 2 Gaddafi da yayansa Faruk daga Abuja ya mika wa amaryar da ya aura a Kano, bisa kyakkyawan zato.

“Ka san sanin masoyi sai Allah. Wani lokaci za ka zauna da mutum shekara da shekaru kana zaton masoyinka ne amma makiyinka ne. Ba kuwa za ka gane haka ba sai ranar da ya yi maka wani abu da ya bayyana. Amana na dauka na ba ta ta ’ya’yana, ita kuma ta rika musguna musu daga karshe ma ta dauki karamin bayan ta doke shi ta sanya shi a Keke-NAPEP, ta kai shi bakin Kasuwar Sabon Garin Kano ta ajiye shi ta yi gaba abinta. Haka yaron ya fada wa jami’an Hisba da suka tsince shi. Ka kuwa san ai yaro ba ya karya,” inji mahaifin.

“Yayana ya fada mini cewa wata mata ce ta zo daga wani gari da yake kusa da Bwari ta ce wata kawarta ta je biki a Rijiyar Lemu, Kano sai ta shiga wani gidan makwbata don a yi mata kunshi, inda wacce ta raka ta gidan take tambayar matar gidan ina yaron da take riko wanda aka tsinta fiye da shekara, ko an samu labarin iyayensa?”

Ya ce matar gidan ta fada wa matar cewa har yanzu ba su ji labarin iyayensa ba, hasali ma har sun sanya shi a makaranta.

Malam Uba ya ce matar ta nemi sanin abin da ya sanya ba a gane iyayen yaron ba. Aka fada mata cewa da yake yaron bai da wayo sosai bai san sunan garinsu ba, abin da dai kawai yake fada shi ne shi daga Tudun Fulani a Abuja yake. Don haka sun yi bakin yin su amma ba su ji labarin iyayensa ba. “Jin haka ya sanya wannan mata ta fara tunanin ai ta san labarin wani yaro da wata kawarta ta taba fada mata cewa dan abokin mijin kawarta da ke Tudun Fulani a Bwari Abuja ya bata, amma da yake ba ta da cikkaken labarin inda abin ya faru sai ba ta zurfafa ba. Bayan wasu kwanaki da dawowarta sai ta je gidan kawarta da ta taba ba ta labarin, inda ta shaida mata abin da ta ji a Kano,” inji shi.

Ya ce take kawar ta tashi ta je Tudun Fulani ta fada wa kawarta, ita kuma ta fada wa mijinta. Shi kuma ya sanya aka sake kiran waya a Kano don sanin sunan yaron. Da jin sunan sai ya tabbatar lallai dan abokinsa ne da ya bata. Daga nan sai ya nemi sanar da shi.

Malam Uba ya ce “Ya yi ta kirana wayata a rufe sai ya kira wayar yayana ya fada masa, shi kuma ya shaida mini cewa an samu wani yaro da aka tsinta a Kano fiye da shekara daya kuma ya ce sunansa Gaddafi, yana jin dana ne. Take zuciyata ta fada mini cewa tabbas Gaddafi ne.”

Kwamandan Hisba na Karamar Hukumar Fagge, Malam Salisu Umar Rijiyar Lemu ya wa Aminiya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce kimanin shekara daya da rabi ke nan da wani mutum da ke aiki a kasuwar Sabon Garin Kano ya kawo wani karamin yaro da aka tsinta yana kuka a bakin kasuwar, bayan da ya firgita mota ta dan taba shi har ya ji rauni. Ya ce bayan sun karbe shi sun je da shi wajen ’yan sanda aka yi masa magani, sannan suka wuce da shi ofishin Hisba na Rijiyar Lemu, inda suka yi masa gyaran targaden da ya samu. Daga bisani suka ci gaba da cigiyar iyayensa amma kwana da kwanaki abin ya ci tura.

“Daga nan sai muka ba da sanarwa a gidajen rediyo da talabijin kuma na dauki hotonsa na sanya a shafin sada zumunta na Facebook amma dai ba a samu iyayensa ba. Don haka sai muka ci gaba da rikonsa a ofishinmu na Rijiyar Lemu,” inji shi.

Ya ce, “Ana cikin wannan hali ne sai wani mutum mai suna Isah Mai’unguwa wanda ba ma’aikacin Hisba ba ne, amma yana zuwa ofishinta don taimaka wa masu sabunta katin dan kasa. A haka sai suka saba da yaron saboda yakan saya masa abinci. Don haka sai ya nemi a ba shi shi ya je ya kwana biyu gidansa. Bayan mun amince ya tafi da shi ya kwana biyu ya maido shi. Daga nan ya sake nuna sha’awar a ba shi rikon yaron ya zauna a gidansa a matsayin da. Bayan mun sanar da Hakimin Fagge da Mataimakin Ciyaman sai muka amince aka ba shi. Sai a makon nan ya zo ofishinmu da mahaifin Gaddafi. A lokacin na je wani taro kuma ya zo mana da yayan Gaddafin mai suna Faruk,” inji shi.

Malam Salisu ya ce Hukumar Hisba ta je har Hotoro ta kamo tsohuwar matar mahaifin yaron da take rikonsa lokacin da ya bace ta tuhume ta da hannu a kan jefar da shi a bakin kasuwa.

“Ko da muka tsinci yaron akwai alamar bulala a wuyansa da ke nuna ba ta zaman lafiya da yaran. Don haka mun je Hotoro mun taho da matar mai suna Maryam. Da muka zo ofis kuma muka fahimci akwai alamun rashin da’a a kalamanta, sai muka ajiye ta a nan ofishinmu sai da ta kwana. Daga bisani bayan tsohon mijin ya ce ya kyale ta da Allah sai muka yi mata nasiha muka sallame ta. Daga nan kuma muka dauki hotuna da yaron da mahaifinsa da kuma yayansa,” inji Malam Salisu.

Ya yi nasiha ga iyaye maza su guji tsallake shari’a wajen kwace ’ya’yansu daga iyayensu mata yayin da suka rabu da su. Ya ce “Mutum ne ya kamata ya bi shari’a ba shari’a ce take bin mutum ba. Ka ga da tun asali da ya rabu da uwar yaran bai kwace su daga wurinta ba, haka ba za ta faru da su ba.”

Ya kuma yi nasiha ga mata masu rikon ’ya’yan da ba nasu ba, su ji tsoron Allah su rika yi wa yaran adalci.

Isah Murtala Ibrahim wanda ake kira da Mai’unguwa wanda ya rike yaron a gidansa har shekara daya da rabi, ya bayyana wa Aminiya cewa: “Ni ba ma’aikacin Hisba ba ne amma nakan je ofishinsu na Rijiyar Lemu don taimaka wa masu katin dan kasa. A nan muka shaku da Gaddafi domin duk lokacin da ya gan ni na zo da safe sai ya rugo ya kama hannuna ya rike yana cewa Ankul ka saya mini abinci yunwa nake ji. Ni kuma sai in ja shi mu tafi wajen mai shayi in saya masa ya sha, haka da yamma.”

Ya ce wata rana da yamma zai tafi gida sai yaron ya rike hannunsa ya ce sai ya bi shi zuwa gida. “Ganin na yi na yi, ya ki yarda sai na koma cikin ofishin na samu Kwamanda na nemi ya amince in tafi da shi gidana ya kwana biyu a yi masa wanka da wanki. Bayan kwana biyu na dawo da shi, sai yaron ya ki yarda ya rabu da ni, wannan ya sa tilas na nemi Hukumar Hisba ta ba ni izinin rike shi a matsayin da har zuwa lokacin da za a samu mahaifansa,” inji shi.

Ya ce, “Bayan cika sharuddan da Hukumar Hisba ta gindaya, suka ba ni rikon Gaddafi, na tafi da shi gida kuma na ci gaba da yawo ina neman mahaifansa. Saboda shi duk wata unguwa da ake kira Tudun Fulani a fadin birnin Kano sai da na san ta amma Allah bai sa na ci nasarar gano mahaifansa ba. Don haka sai muka yanke shawara ni da matata ta sanya shi makaranta tare da sauran yarana. Ko a ranar da mahaifinsa ya zo nan tare da yayansa mai suna Faruk, can a makaranta muka samu Gaddafin, sun fito tara, na je na kirawo shi tare da ’yata suka fito. Da fitowarsu bakin kofar makarantar, babansa ya hango shi sai ya fashe da kuka. Haka suka yi ta kuka manya da kanana.”

Ita ma da take nuna jin dadinta na gane danta, mahaifiyar Gaddafi mai suna Shafa ta fara ne da godiya ga Allah da ya bayyana dan cikin koshin lafiya tare da yin godiya ga Malam Salisu Mai’unguwa da Hukumar Hisba ta Kano kan kokarinsu a wannan lamari.

“Na fada cikin mummunan tashin hankali har sai da ya so ya shafi lafiyar idona. Cikin taimakon Allah dai ga shi an gane shi. Don haka ina cikin murna wacce har ma ta yi min yawa. Ba abin da zan ce sai godiya ga Allah da Ya dawo mini da shi,” inji ta

Duk yunkurin da Aminiya ta yi na jin ta bakin Maryam, tsohuwar matar mahaifin yaron da ake zargi da jefar da yaron ta ci tura. Lokacin da wakilinmu ya same ta a tarho, ta ki yarda ta ce komai kan lamarin kuma har zuwa lokacin kammala wannan rahoto ta ki amsa sakon waya da ya aika mata.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya