✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata ta nema wa mijinta amarya lokacin da ta dauki ciki

Duniya mai abin mamaki, a lokacin da wadansu matan auren ke hallaka mazansu saboda karin aure, sai ga wata ta nema wa mijinta kishiya saboda…

Duniya mai abin mamaki, a lokacin da wadansu matan auren ke hallaka mazansu saboda karin aure, sai ga wata ta nema wa mijinta kishiya saboda abin da ta kira ba ta son ta ga ba ya samun kula sakamakon samu juna biyu da ta yi.

Akasari dai mata ba su taba amincewa mijinsu ya kara aure, idan kuwa ya kara to zai ga ba daidai ba, idan ko magana ya yi da wata sai su fusata. A koyaushe suna kallon kishiya a matsayin wata annoba ce a rayuwar aurensu. Sai ba dukkan mata ba ne suke da irin wannan tunani ba.

Kwanakin baya ne aka samu rahoton wata mata ’yar kasar Malesiya ta nema wa mijinta amarya lokacin da ta samu juna biyu. Ta ce ta dauki wannan kudiri ne don guje wa wahalar rashin kula da mijinta zai fuskanta saboda juna biyun da take da shi kuma wannan larurar ba za ta ba ta damar cikakkiyar kula da mijinta ba.

Wannan lamarin ya faru ne a garin Shah Alam a kasar Malesiya lokacin da  matar mai suna Khuzatul Atikah, ta fara nema wa mijinta Samuel Dzul, amarya lokacin da ta samu juna biyu. Khuzatul ta fahimci cewa, mai gidanta yana cikin damuwa kasancewar bayan ya dawo daga aiki sai ya zo ya fara wasu ayyukan gida, inda ganin hakan ta fara tausaya masa kan irin ayyukan da yake yawan yi ga shi tana fama da rashin cikakkiyar lafiya saboda cikin da take dauke da shi.

Saboda tsananin soyayyar da Khuzatu ke yi ga mijinta, ba ta son ta ga ya wahala ko ya rasa samun cikakkiyar kula, wannan ne babban dalilin da ya sa ta fara nema wa mijinta amarya saboda gazawarta ga yin wasu harkokin da ta saba yi wa Samuel Dzul.

A lokacin da Khuzatu, ta tambayi mijinta yana bukatar karin mata sai kawai ya yi murmushi, wanda hakan ya nuna ya yi na’am da bukatar matar ke nan.

Khuzatu, ta yi kokarin nema wa mijinta matar da za ta zamar mata kishiya hakan ya sa ta yi sa’ar samun wata budurwa mai suna Nur Fathonah don ta auri mijinta.

Bayan Khuzatu, ta nemo amaryar da ta dace da mijinta wanda hakan zai sa ta zamar mata kishiyarta. A lokacin Nur Fathonah ta samu sakon Khuzatu, na ta auri Samuel, wanda hakan ya ba ta matukar mamaki har ta ce ba ta taba tunanin irin wannan auren zai yiwu ba. Daga bisani sai ta amince da bukatar Khuzatu na ta auri mijinta.

Bayan aure Samuel, yana cikin kwanciyar hankali da annashuwa da matansa biyu kamar yadda uwargida Khuzatul Atikah take buri kuma ta ce, ta dace da abokiyar zama daidai da irin wanda take bukata. A yanzu duk suna gudanar da harkokinsu tare da kuma biya wa mijinsu bukatarsa, yayin da suke taimaka wa Samuel wajen sana’arsa ta nadar bidiyo da tarbiyyar ’ya’yansu da sauransu.

Wannan labarin ya zama darasi ga sauran ma’aurata, ganin soyayyar miji da mata da idan har namiji yana bukatar karin aure sai dai ya nemi aurensa ba tare da amincewar uwargida ba.