✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata uku sun haifarwa dan kwallon City jarirai uku a tsakanin makonni 6

Wani abu mai kama da almara ya faru da dan kwallon Stoke City da ke Ingila Saido Berahino  bayan jaridar  The Sun ta Ingila a…

Wani abu mai kama da almara ya faru da dan kwallon Stoke City da ke Ingila Saido Berahino  bayan jaridar  The Sun ta Ingila a ranar Litinin da ta wuce ta ruwaito  yadda dan kwallon ya yi wa wasu mata uku ciki a lokuta daban-daban ba tare da sanin kowaccensu ba kuma suka haifar masa jarirai a tsakanin makonni 6.

Saido wanda asalin iyayensa sun fito ne daga Bujumbura na Burundi amma suka haife shi a Ingila, an shaide shi manemin mata ne.  Kuma duk wadannan mata da suka haifar masa wadannan jarirai, ya yi haka ne ba tare da ya aure su ba.

Berahino wanda yake da shekara 25, ya yi wasa a kulob da dama, ciki har da kulob din West Brom Albion.  Kuma yanzu haka yana wasa ne a kulob din Stoke City.

Sannan ya yi wa Ingila wasa a matakai daban-daban a kulob din matasa, amma bai taba buga wa babbar kungiyar kwallon kafa ta Ingila ba.

Rahoton ya nuna cewa da farko wani Lauya ne ya gabatar da bayanin yadda wasu mata biyu suka haifar wa Berahino jarirai biyu a lokuta daban-daban a takardun haihuwar jariran da dan kwallon ya sanya wa hannu a matsayin mahaifinsu.

Takardar haihuwar farko ta nuna an haifar masa jaririn ne a ranar 30 ga watan Mayun, 2018 yayin da takarda ta biyu ta nuna an haifar masa jaririn ne a ranar 17 ga watan Yulin bana.  Ana cikin haka ne sai Lauyan wata mata shi ma ya gabatar da wata shaida da ta nuna jaririn da matar ta haifa na Berahino ne, kuma ta haife shi ne a ranar 15 ga watan Yulin wannan shekara.

Wannan dalili ne ya sa dan kwallon ya zama abin zunde musamman a jaridun Ingila, inda aka rika zolayarsa da  cewa ya samu nasarar haihuwar jarirai uku a tsakanin makonni 6 maimakon mayar da hankali wajen zura kwallaye uku a raga a lokacin da yake kwallo.