✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mataimakin dan ta’addan Binuwai Gana ya shiga hannu

Rundunar Sojin Najeriya ta damke mataimakin Terwase Akwaza, wanda aka fi sanda da Gana, babban dan ta’addan jihar Binuwai da sojoji suka bindige a kwanakin…

Rundunar Sojin Najeriya ta damke mataimakin Terwase Akwaza, wanda aka fi sanda da Gana, babban dan ta’addan jihar Binuwai da sojoji suka bindige a kwanakin baya.

Kwamadan Rundunar ta Musamman da ke Doma, Jihar Nasarawa, Manjo Janar Ali Mounde ya gabatar da Kumaor Fachii a gaban ’yan jarida.

“Mun damke Fachii ne a Karamar Hukumar Katsina Ala, Jihar Binuwai a lokacin da yake tare da budurwarsa.

“Gana da ’yan kungiyarsa sun tayar ad hankalin jama’a a Jihar Binuwai da makwabtanta a shekaru biyar da suka wuce.

“Bayan mutuwarsa an yi ta hasashen cewa ya mika shugabancin kungiyar ga mataimakinsa, Kumaor Fachii”, inji shi.

Da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a ofishin rundunar, Fachii ya ce, “Ni dan kungiyar Gana ne amma ba ni ba ne mataimakinsa”.

A watan Satumba ne sojoji suka bindige Terwase Gana bayan sun kama shi a hanyar zuwa Makurdi tare da wasu yaransa inda gwamantin jihar ta ce za su je ne domin karbar afuwa.

Sai dai ko a lokacin, sojoji sun ce sun kashe shi ne a musayar wuta da suka yi a lokacin da suka kama shi.