✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mataimakin Shugaban kasar Kenya ya gurfana a Kotun duniya

Mataimakin Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya karyata tuhumar da ake yi masa, ta haddasa rikicin bayan zabe a kasar Kenya shekara biyar da ta…

Mataimakin Shugaban kasar Kenya, William RutoMataimakin Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya karyata tuhumar da ake yi masa, ta haddasa rikicin bayan zabe a kasar Kenya shekara biyar da ta gabata, a zaman share fage na shari’ar da kotun ICC ta fara yi masa.
An fara wannan shari’a ne a birnin Hague, tare da tuhumar  Ruto da Shugaban gidan Rediyon Kenya Joshua Arak Sang, inda aka tuhume su da laifin keta haddin dan Adam. daukacin mutanen dai sun amsa cewa “ba su aikata laifukan da ake tuhumarsu ba,” kamar yadda suka bayyana wa Alkali Chile Eboe-Osuji.
Ruto ya halarci zaman kotun ne a kashin kansa, don amsa tuhumar laifin tada rikicin bayan zaben Shugaban kasa na shkarar 2007. Gungun ’yan majalisar Kenya da magoya bayansa ne suka tarbi Ruto a lokacin da ya isa kasar don ya gurfana a gaban kotu.
Shi ma Shugaba Uhuru Kenyatta, wanda a da tsohon abokin adawar Ruto ne, kuma yanzu ga su a inuwar siyasa guda, duk za su fuskanci hukunci a ranar 12 ga watan Nuwambar bana.
Wannan kotu ta ICC tana samun matsin lamba daga kasashen Afirka 54, kan yadda take hukunta mutanen nahiyar, don haka ta bukaci ta yi watsi da tuhumar da take yi wa shugaban kasar Kenya.