Search
Subscribe
Mataki na gaba: Daga Uwargidan Shugaban Kasa zuwa Mace ta Farko

Mataki na gaba: Daga Uwargidan Shugaban Kasa zuwa Mace ta Farko

A ranar Alhamis din makon jiya ne matar Shugaban kasa Hajiya A’isha Buhari ta sanar da cewa ta fi so a rika kiranta da Mace ta Farko a Najeriya (First Lady of Nigeria) maimakon Uwargidan Shugaban Kasa da ake kiranta da shi a lokacin wa’adin mulkin mijinta na farko.

Hajiya A’isha dai ta bayyana haka ne a yayin da take jawabi a wajen wata liyafa da ta shirya wa matan gwamnoni masu barin gado da kuma sababbi.

Hajiya A’isha ta yi nuni da cewa, “Lokacin da aka zabi maigidana a karo na farko ni da kaina na zabi a rika kirana da Uwargidan Shugaban Kasa, amma yanzu na fahimci cewa hakan ya haifar da rudani a jihohi, inda aka rika tababar shin za a rika kiran matar Gwamna da sunan Uwargudar Gwamna ne ko kuwa Mace ta Farko a jihar? Saboda haka ina so (matan gwamnoni) ku yafe mini saboda rudanin da na haifar muku tunda farko, amma daga yanzu na zabi  a rika kirana da Mace ta Farko a Najeriya.”

Sai dai kuma shi kansa Shugaban Kasa Buhari ya taba fitowa fili a wata hira da aka yi da shi a jaridar “Daily Trust “ a shekarar 2015, inda ya ce ba zai amince da matsayin Mace ta Farko ba, domin babu wannan matsayin a tsarin mulkin Najeriya, amma yanzu ga dukkan alamu Madam ta canja wannan matsayin nasa kuma canjin ya zauna.

A yayin da Hajiya A’isha ke kokarin kawar da rudani ga matan gwamnoni, sai dai kuma ga dukkan alamu yanzu ne ma ta haifar da rudanin a gare su, domin akwai jihohi da dama da gwamnoninsu ke da mace fiye da daya, idan kuma Gwamna ya ayyana guda a cikinsu ya ce ita ce Mace ta Farko, rikici zai tashi saboda sauran za su ce ba su yarda ba domin dukkansu matansa ne, an sha samun irin wannan matsalar a shekarun baya.

Amma da gwamnatin Buhari ta zo da tsarin amfani da sunan Matar Shugaban Kasa, a jihohi ma sai aka rika amfani da Matar Gwamna. Saboda haka ba a samu wata matsala ba, domin kowace daga cikin iyalin Gwamna matarsa ce, don haka tana iya fitowa da wani shirin da take son aiwatarwa domin inganta rayuwar jama’a.

Matsayin Mace ta Farko ya fito karara ne a zamanin mulkin Shugaban Kasa Ibrahim Badamasi Babangida, lokacin da mai dakinsa marigayiya Maryam Babangida ta fito da shirinta mai suna “Shirin Inganta Rayuwar Matan Karkara”  (Better Life for Rural Women). A wancan lokacin ta rika fitowa tana gudanar da harkokinta wanda ya sanya a kullum ake jin duriyarta, sai dai kuma ita duk harkokinta tana yi da mata ne kawai, wato ita da matan gwamnonin jihohi, ba ta shigo da maza ba. Idan akwai wani abu da za ta yi a wata jiha, idan ba za ta samu damar halarta ba, matar Gwamna take sanyawa ta wakilce ta ko wata Minista mace.

Amma da zamaninta ya shude, matar Shugaban Kasa Janar Abacha Hajiya Maryam Abacha ta shigo, sai al’amarin ya kara bunkasa, domin mulkin da Maryam Abacha ta shimfida ya ninka na Maryam Babangida nesa ba kusa ba, domin kuwa a zamaninsu maigidanta Janar Abacha ne kawai ba ya karkashin ikonta. Tana da iko da duk manyan jami’an gwamnati.

Bayan shudewar gwamnatinsu sai Allah Ya kawo gwamnatin Janar Abdulsalam Abubakar, amma da yake watanni goma sha daya kawai ya yi a mulki, matarsa Fati Lami Abubakar, wacce mai shari’a ce, ba ta samu damar mike kafa sosai ba, sai aka mika mulki ga farar hula inda Shugaba Obasanjo ya shigo.

A zamaninsa matarsa marigayiya Stella Obasanjo ta ja zarenta, domin ta yi mulki daidai iyawarta, a lokacinta ta fito da tsarin ado da siket da ake kira Stella, wanda har yanzu mata ba su daina yayinsa ba. Mijinta bai kammala wa’adinsa ba sai Allah Ya karbi ranta.

Bayan Obasanjo ya sauka sai marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa ya shigo da matarsa  Hajiya Turai, ita ma ta baza mulki a zamaninta, amma sai Allah Ya karbi ran mijinta kafin ya sauka.

Daga nan sai Mataimakinsa Goodluck Ebele Jonathan ya haye karaga, inda matarsa  Patience Jonathan ta samu damar shimfida nata irin mulkin, inda suka yi shekara shida suna damawa.

A shekarar 2015 Allah Ya kawo Shugaba Buhari, wanda ya fito fili ya ce ba zai yarda da wannan tsarin ba, saboda haka sai aka rika kiran matarsa da Uwargidan Shugaban Kasa ko Matar Shugaban Kasa kawai, kuma ana cikin tafiya sai ita ma ta fito da shirinta mai suna “Kyautata Rayuwa Domin Gaba” (Future Assured), daga nan sai aka wayi gari al’amarin ofishin Matar Shugaban Kasa sai kara gawurta yake yi. Saboda haka da maigidanta ya samu damar ci gaba da mulki a karo na biyu sai ta ga ta dace ta fito fili ta gudanar da harkokinta kamar yadda wadanda suka gabace ta suka yi.

Abin tambaya shi ne, shin da amincewar Shugaba Buhari ne Madam ta canja wannan suna ko kuwa ita ce ta yi gaban kanta? Idan kuma da saninsa ne, wannan yana nufin ya canja ra’ayinsa ne ko kuwa yanzu shi ma ya gane cewa ya haifar da rudani ne? Jama’a dai sun zura ido suna jiran su ji abin da Shugaba Buhari zai ce game da warware maganarsa da mai dakinsa ta yi a ranar Alhamis din makon jiya.

Kodayake an ce a tsarin soja matar soja ta fi shi mukami da mataki guda, wato idan igiya daya mijinta yake da shi, ita kofur ce mai igiya biyu. Watakila abin da ya faru ke nan, wato sawun giwa ya take na rakumi.

Muna fata Hajiya za ta gafarci Hausawa idan ta ji suna ci gaba da kiranta da Uwargidan Shugaban Kasa, domin a tsarinsu babu ‘Mace ta Farko da Hausa sai dai a ce Uwargida domin a cikin gida ita ce shugaba.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin