Da Dumi Dumi

Matar da ke auren maza biyu ta shiga hannu

Ana zargin wata mata mai suna Hauwa Aliyu mai shekara 26 da ke zaune a Unguwar Mariri a Karamar Hukumar Kunbotso a Jihar Kano da auren maza biyu a lokaci guda.

Aminiya ta samu labarin cewa Hauwa ta auri mijinta na farko ne mai suna Muhammad Bello tsawon shekara 19, inda suka haifi ’ya’ya shida daga bisani kuma ta kara auren wani mai suna Bala Abdussalam shekara daya da watanni da suka gabata, inda suka haifi da daya.

 

Mijina na farko ya ce ya sake ni -Hauwa

Sai dai da take yi wa Aminiya karin haske matar wadda ’yar asalin garin Magatawa ce ta ce ta auri mijinta na biyun ne bayan da mijinta na farko ya furta cewa ya sake ta. “Muna zaune da mijina tsawon shekara 19 ’ya’yanmu shida. Wata rana muka yi fada ya fada min ya sake ni. Bayan ya sake ni sai na zauna a gidansa don yin iddata. Bayan na gama idda sai ya fara rashin lafiya inda ya koma kauyensu don neman magani,” inji ta.

ADVERTISEMENT

Ta ce tana zaune cikin wannan hali ba mai daukar nauyinta da na ’ya’yanta tsawon watanni sai ta hadu da sabon mijinta wanda  tsohon saurayina, “Sai na ga sauki ne a gare ni, domin ko ba komai zan samu mai taimaka min wajen kula da ’ya’yana, don haka na amince muka yi aure har ga shi Allah Ya ba mu da guda daya,” inji ta.

Ta kara da cewa:  “Lokacin da tsohon mijina ya sake ni na fada ’yan uwana saboda ni marainiya ce, to sai suka ce in bayar da shaida na fada musu cewa bai ba ni ba. Haka  a lokacin da batun auren ya taso na je na sanar da su, amma ba su goyi bayan auren ba bisa tsoron kada mijina na baya ya dawo ya musanta sakin. Don haka ba su shiga batun auren ba, sai muka samu wadansu mutane a unguwar suka daura mana aure bayan ya biya sadakin Naira dubu 20.”

Hauwa Aliyu ta nanata cewa tsohon mijinta ya sake ta domin da kansa ya nanata haka a lokacin da ya zo ya iske sabon mijinta a gidansa. “Shi da bakinsa lokacin da ya zo ya tarar da sabon mijin nawa a gaban mutane ya ce ya san ya sake ni. Amma shi yana neman dalilin da ya sa na kawo masa wani kato nake zaune da shi a cikin gidansa,” inji ta.

Game da zamansu da sabon mjin a gidan tsohon mijin, Hauwa ta ce, “Ni ma da kudina aka gina wasu sassan gidan da muka tare ba a karasa wasu wurare ba ni na yi amfani da kudina aka yi filastar dakinmu sannan na haka shadda da rijiya kuma na gina dakin yara guda daya da sauran ayyuka a gidan.”

Da Aminiya ta tambayi matar idan aka ba ta zabi a tsakani mazan biyu da sauri ta amsa cewa mijinta na biyu za ta zaba.

 

Aure muka yi da ita – Sabon mijin

Bala Abdussalam shi ne sabon mijin, ya ce iya saninsa matarsa sun rabu da tsohon mijinta, hakan ya sa ya nemi aurenta inda har suka samu da. “Abin da na sani ta fada min cewa mijinta ya sake ta don haka na nemi aurenta na biya sadaki aka daura mana aure.’

Da Aminiya ta tamabye shi dalilin da ya sa suka ci gaba da zama a gidan tsohon mijin sai ya ce, “Ita ta nuna min ita da mijinta suka gina gidan don haka tana da ikon sanya kowa a ciki. Da farko na so mu je mu kama gidan haya amma ta nuna min cewa dawainiya za ta yi min yawa don haka muka tare a gidan. Ban san da maganar wani aure a kanta ba sai lokacin da tsohon mijinta ya zo ya same ni a gida ya dauko tabarya zai kwada min. Allah Ya taimake ni na yi karfin hali na kwace inda kuma ya yi min bayanin cewa har yanzu shi bai saki matarsa ba.”

 

Ban saki matata ba – Tsohon mijin

Da yake mayar da jawabi toshon mijin Malam Muhamamd Bello ya ce bai taba sakin matarsa ba, abin da kawai ya sani ya je gida neman magani. “Ban saki matata ba. Na dai kamu da rashin lafiya, na tafi gida neman magani kuma a lokacin da zan tafi sai da na nemi in tafi da ita da ’ya’yana amma ta ki, ta ce ba za ta iya zaman kauye ba, don haka na tattara na tafi. Duk da cewa na dade ban zo ba, amma hakan ba ya nufin na sake ta. Sai kwanan nan da na zo gidan sai na tarar da wani kato a kan gado yana kwance. Na tambaye shi ko shi wane ne ya ce wai shi ne mijin matata. Allah ne Ya tsare ban fasa masa kai da tabarya ba.  Don haka a bincika a fada min yadda abin ya kasance. Ni kuma wallahi ban sake ta ba.”

Malam Bello ya musanta cewa akwai kudin matarsa a ginin gidan. Har ila yau ya nemi hukuma ta bi masa hakkinsa domin shi yana nan a kan bakarsa cewa Hauwa matarsa ce bai sake ta ba.

 

Za mu tura su kotu -Hisbah

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Darakta Janar na Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Dokta Aliyu Musa Aliyu Kibiya ya ce dukkan mutanen suna hannunsu kuma da zarar sun kammala hada bayanai za su gurfanar da su a gaban kotu.

“Lura da sarkakiyar da lamarin ke da shi za mu tura mutanen ga kotu don shari’a ce kadai za ta iya warware wannan lamari idan ta gudanar da bincike,” inji shi.

Shugaban ya yi kira ga al’ummar Musulmi su kiyaye  dokokin Allah  tare da kiyaye dangantaka a tsakaninsu lura da muhimmancin da hakan ke da shi a rayuwar jama’a.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya