✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar da ta kona gaban mijinta ta shiga hannun ’yan sanda

Yan Sanda a Jihar Kano sun kama wata mata mai shekara 35 mai suna A’isha Ali bisa zarginta da watsa wa mijinta tafasasshen ruwa a…

Yan Sanda a Jihar Kano sun kama wata mata mai shekara 35 mai suna A’isha Ali bisa zarginta da watsa wa mijinta tafasasshen ruwa a al’aurarsa.

Wacce ake zargin an ce ta kona wa mijinta mazakuntarsa ce saboda yana son ya yi mata kishiya.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya tabbbatar wa manema labarai faruwar haka, inda ya ce sun kamo matar a garin Babura da ke Jihar Jigawa. Ya ci gaba da cewa wadda ake zargin a halin yanzu tana Sashen Binciken Manyan Laifuffuka (CID) tana amsa tambayoyi, inda daga bisani za su gurfanar da ita a gaban kotu bisa zargin yunkurin hallaka mjinta.

Aminiya ta gano cewa wacce ake zargin ta antaya wa mijinta Malam Aliyu Ibrahim Fayan-Fayan ruwan zafi ne a gabansa bayan ta gano yana shirin yi mata kishiya. Rundunar ’Yan sandan ta tabbatar da cewa mutumin ya samu mummunar kuna a gabansa kuma a yanzu yana kwance a Babban Asibitin  Dambatta, yana jinya.

Kakakin Rundunar ya ci gaba da cewa wacce ake tuhumar ta tsallake zuwa wani kauye a Kano, bayan da ta aikata wannan aika-aika kuma daga bisani ta arce zuwa Babura, inda a can ne ’yan sandan Operation Puff Adder suka kamo ta.

“Kwarya-kwaryar binciken da muka gudanar ya nuna cewa ta aikata wannan mugun abu ne saboda ta ji mijinta zai kara aure. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, Alhaji Iliyasu Ahmed shi ne ya ba da umarnin mayar da binciken wannan zargin laifi zuwa CID. Sannan muna sa ran za mu gurfanar da ita a gaban kotu da zarar mun gama bincike,” inji DSP Kiyawa.

Daga karshe ya yi kira ga sauran ’yan kasa nagari da su rika ba da rahoton duk wani abu da ya auku cikin gaggawa ga ofishin ’yan sanda mafi kusa, domin haka ne kawai zai sanya a iya kama wadanda suka aikata laifin cikin gaggawa tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban kuliya.