✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar da ta kulle ‘yar aikinta a bandaki ta shiga hannu

Wata mata mai kimanin shekara 35 mai suna Mabel Okechuku ta shiga komar ‘yan sanda a Jihar Legas bayan da aka zarge ta da laifin…

Wata mata mai kimanin shekara 35 mai suna Mabel Okechuku ta shiga komar ‘yan sanda a Jihar Legas bayan da aka zarge ta da laifin rufe ‘yar aikinta a bandaki ta yi tafiyarta coci, lamarin da ya sanya wasu da ke makwabtaka da ita suka yi kararta ga hukumar ‘yan sandan da ke yankin Baruwa a jihar.

Makwaftan matar wadanda suka shigar da karar sun shaida wa Aminiya cewa matar na yawan azabtar da yarinyar, inda take kulle ta a bandaki a duk lokacin da zata fita daga gidan. Sai dai matar Mabel Okechuku ta musanta zargin da ake mata, ta ce ta azabtar da yarinyar ce ta hanyar tsare ta a bandaki domin taki bin umarninta, na kin shirya wa da wuri su tafi coci.

Ta kara da cewa ta shirya zuwa coci da yarinyar, amma sai yarinyar ta ki maida hankali ta shiga bandaki ta yi zamanta, hakan ne yasa da ta fusata ta garkame ta a ciki.

Kururuwar yarinyar ne ya ja hankalin makwabtan nata, suka shiga gidan suka tarar da yarinyar mai shekaru 14 rufe a bandaki, suka karya kofar suka fitar da ita, inda suka same ta da alamun duka a jikinta, kafin daga bisani ‘yan sanda su kame matar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas, Edigal Imohimi ya ba da tabbacin cewa za a gurfanar da wanda ake zargi a kotu nan ba da jimawa ba da zarar sun kammala bincike.