Da Dumi Dumi

Matar da ta kulle yaro a cikin akurkin kare ta shiga hannu

Rundunar ‘yan sandan Legas tayi nasarar kame matar nan da fefan bidiyon ta ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta na zamani inda aka ganta ta fito da wani yaro daga kejin karnuka tayi ta jibgar sa da tsumagiya kafin daga bisani ta tasa keyarsa cikin akurkin karnukan ta rufe shi a ciki.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya aike wa Aminiya ya shaida cewa tun bayan bazuwar fefen bidiyon matar jami’an ‘yan sandan Legas da ke aikin a sashin yaki da cin zarafin mata da yara suka himmatu dan ganin an ceci yaron dan shekara 10 tare da kame matar domin ta fuskanci shari’a.

Ya ce, a jiya ne dakarun rundunar suka yi nasarar kame matar mai suna Onyinye Mbadike mai shekaru 24 a gidanta da ke yankin Aguda a Legas ana zarginta ne da cin mutumcin yaro karami Chibike Ezi Amaka, “Jama’a da dama sun yi Allah wadai da fefen bidiyon da ya nuna matar na cin zarafin yaron, an ga lokacin da ta fito da shi daga cikin kejin karnukan tayi ta tsala masa tsumagiya kafin daga bisani ta mayar da shi cikin kejin ta rufe, ta amsa laifin ta kuma tabbatar da cewa, ita ce a fefan bidiyon amma ta musanta cewa ta rufe yaron da karnuka tace a akurkin da ta rufe yaron shi kadai ne babu karnuka a ciki, jami’an mu sun ceto yaron za kuma a gurfanar da matar a gaban kotu domin ta fuskanci hukunci” in ji shi.

DSP Bala, ya ce binciken da suka yi ya tabbatar masu da cewa yaron dan uwar matar ne, mahaifin sa yaya ne gare ta, mahaifiyar ta ce ta kawo shi wajenta riko ne daga jihar Anambra tare da ‘yan uwan sa mata biyu a shekarar 2012 bayan da mahaifan yaron suka rasu.

Wacce ake zargin ta bayyana dalilanta na cin zarafin yaron da cewa, ya dauki giya a firji ya sha ya fita hayyacin sai ya yi ta yi mata fitsara a cikin gida hakan ya sanya ta kulle shi a akurkin domin yi masa horo.

ADVERTISEMENT
Share