✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar da ta shekara 16 a keken guragu tana neman dauki

Uwani Muhammed, mai shekaru 38 da haihuwa da ke zaune a Unguwar Sabon Fegin Malam Inna a Jihar Gombe ta gamu da tsautsayin da yanzu…

Uwani Muhammed, mai shekaru 38 da haihuwa da ke zaune a Unguwar Sabon Fegin Malam Inna a Jihar Gombe ta gamu da tsautsayin da yanzu haka ta share fiye da shekara 16 tana rayuwa a keken guragu.

Da take zantawa da Aminiya a gidansu, Uwani Muhammed ta bayyana yadda ta samu wannan larurar jinya da ta samu kanta tsawon lokaci, cikin hawaye ta ce tuntube ta yi a gidan mijinta da daddare, sai ta fadi, a lokacin shekara hudu da aurenta, kuma kafin wannan lokacin ne ta haifi ‘yarta guda daya.

Uwani, ta ce daga nan ne aka kai ta Asibitin Sunnah dake Gombe, inda aka gaza gano aslin ciwon da ya same ta. Daga nan aka sake kaita Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya dake Gombe, anan ne suka tura ta Asibitin Koyarwa na JUTH dake Jos, anan ne aka yi mata gwajin MRI Spine, inda aka gano matsalar amma aka ce ba za a iya mata magani a Najeriya ba sai sun je kasar waje.

Ta kara da cewa an ce sai sun je kasar waje kuma ga shi ba su da kudi, “an yi min wannan gwajin ne a ranar 5 ga Watan Janairun 2010, amma sai a Watan Disamban 2017 muka samu tallafi daga al’umma bayan wani Bawan Allah ya sanya hotona a Facebook, na samu tallafi daga jama’a har na Naira miliyan hudu muka je Kasar Moroko.

“A Moroko aka yi min aiki na farko aka sanya min wani tiyo a gadon bayana, wanda yake zuke wani ruwa (Fluid) da yake taruwa a wani waje da ya bar hanyarsa, aka ce mu sake koma bayan wata shida a cire tiyon, sannan a yi min aiki karo na biyu. To amma tun karshen Watan Agusta wa’adin ya kare, ba mu da kudin komawa a yi aikin, don haka yanzu abinda muke nema ya kai Naira Miliyan 2 da dubu 370, amma har ga Allah ba mu da wannan kudi yanzu,” inji ta.

To amma sai dai majinyaciyar ta yi amfani da wannan damar, tana mai rokon gwamnati da masu hali da su kawo mata dauki domin ceto rayuwarta daga wannan doguwar jinya da ta shafe sama da shekara 16 tana fama, don komawa Kasar Moroko a cire mata wannan tiyo da aka sanya mata a gadon bayanta, tana mai cewa idan ya jima a jikinta kila zai yi mata illa. Ta ce a baya gwamnati ta taimaka mata, amma taimakon ba mai yawa ne sosai ba.

Uwani ta kuma shaida wa wakilinmu cewa ta gamu da wannan larura ce a gidan mijinta, amma tun daga lokacin zuwa yanzu a gidan iyayenta take, kuma su ke kula da ita, domin tuni mijin nata ya sake ta a cewarta.

Daga nan ta kara da cewa tun bayan dawowar ta daga Moroko kullum tana zuwa gashin kashi a Asibitin Koyarwa Na Gwamnatin Tarayya dake Gombe, sai dai kungiyar IMAN sun tallafa mata wajen biyan kudin gashin kashin da ake yi mata.

Daga nan ta roki al’umma da su taimaka mata musamman ma.

Da Aminiya ta ziyarci Ma’aikatar Mata da Walwalarsu ta Jihar Gombe, ta samu jin ta bakin Mukaddashin Babban Sakataten Ma’aikatar, Suleiman K.M Doho, inda ya ce ba su taba jin labarinta ba, amma za su nemi ta rubuto don nema mata taimako daga gwamnati.