✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Davido ta kamu da cutar Coronavirus

Matar shahararran mawakin nan na Kudancin Najeriya wato Davido ta kamu da cutar Coronavirus. Mawakin ne ya sanar da hakan a shafinsa na twitter a…

Matar shahararran mawakin nan na Kudancin Najeriya wato Davido ta kamu da cutar Coronavirus.

Mawakin ne ya sanar da hakan a shafinsa na twitter a ranar Juma’a 27 ga watan Maris 2020, ya ce matarsa Chioma da dansu dan jariri sun dawo daga wata tafiya daga kasar Birtaniya, yayin da shi ya dawo daga Amurka sun kuma fasa wani balaguro da suka shirya yi biyo bayan barkewar annobar coronavirus.

Davido, ya ce kasancewar tafiyar da suka yi a baya a kasashen da annobar tayi kamari shi ya sa suka ga dacewar suyi gwaji, inda gwajin ya nuna Chioma na dauke da cutar, yayin da shi da dan nasu basu dauki cutar ba.