Da Dumi Dumi

Matar Firayiministan Japan na adawa da nukiliya

Uwargidan Firayiministan Japan na adawa da makamashin nukiliya, don haka ta bayyana ra’ayinta kan cewa bai kamata gwamnatin mijinta ta rik ahankoron kai irin wannan fasahar zuwa kasashen waje.
Misis Akie abe., uwargidan Mista Shinzo Abe, ta bayyana cewa tunaninta ya saba wan a gwamnatin kasar, don haka ta fifita bukatar ganin a bi sababbin dabarun kimiyya da kere-kere wajen samar da makamashi.
“Ina jin takaicin yadda kasar Japan ke kokarin sayar da fasahar kafa tashar samar da makamashin nukiliya a kasashen waje, saboda ina adawa da nukiliya,” injita. Ta jadadda wannan manufa  ne a wani taron sirri da ta yi da kungiyoyin da ke tallafa wa manoma a kasar.  A cewarta: “Na san cewa wannan kimiyyar kere-kere ce managarcfiya da kasar Japan ke da ita,” kamar yadda aka baza a wani shafin sadarwa na wadanda suka shirya taron.

Share