✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Tafawa Balewa da ta rage ta rasu

Allah ya yi wa matar Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Balewa rasuwa, wannan ita ce matarsa da ta rage a duniya cikin matansa hudu. Hajiya…

Allah ya yi wa matar Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Balewa rasuwa, wannan ita ce matarsa da ta rage a duniya cikin matansa hudu.

Hajiya Jummai ta rasu ne a ranar Lahadi da yamma a birnin Legas, kamar yadda daya daga cikin iyalan Marigayi Firaiminista Tafawa Balewa ya tabbatar wa manema labarai.

Daya daga cikin ‘yar Firaiministan, Hajiya Yalwa, ta bayyanawa majiyarmu cewa, “Hajiya Jummai Abubakar Tafawa Balewa ta rasu a Legas. Sannan a yau Litinin za a kai gawar jihar Bauci don yi mata jana’iza.”

Hajiya Jummai ta rasu ne tana da shekara 85 a duniya.