✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Tinubu ta nemi guraben aiki wajen Fashola 

Sanata Oluremi Tinubu, daga mazabar jihar Legas a APC, ta roki da a bata guraben ayyuka daga Tsohon Ministan Ayyuka, Makamashi da Gidaje, Babatunde Raji…

Sanata Oluremi Tinubu, daga mazabar jihar Legas a APC, ta roki da a bata guraben ayyuka daga Tsohon Ministan Ayyuka, Makamashi da Gidaje, Babatunde Raji Fashola. 

Sanatar, wadda mai dakin jagoran jam’iyar APC ce, wato Bola Ahmed Tinubu, ta gabatar da bukatar a yau, yayin zaman Majalisar Dattawan dan tantace wadanda za a nada mukaman ministoci.

“Ka tuna a lokacin wa’adinka na Minista da ya gabata, ban samu damar samarwa wasu ‘yan mazabata Ayyukan Gwamnati ba. Dan haka, in ka sake koma wa a wannan karon, to fa ka tuna cewa, mu ‘yan majalisar dattijai muna da mabukata  daga mazabunmu wadanda ke bukatar mu samu musu ayyuka.” In ji Misis Tinubu.