Matasa 4 sun yi wa ya da kanwa fyade a Bauchi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta kama wasu matasa hudu da suka yi wa ’yan gida daya – yaya da kanwa fyade.

Mai Magana da yawun Rundunar, Ahmed Wakil, ya mahaifin yaran da ke garin Karofin Madaki a jihar ne ya kawo wa ’yan sanda kara.

Ya ce matasan maza guda hudu sun yi wa ’ya’yan nasa fyade ne a kauyen Sabon Kaura.

Wakil ya ce yanzu haka ana tsare da matasan inda ake kan bincike kafin ta gurfanar da su gaban kuliya.

Sanarwar da ya fitar ta ce rundunar ta kuma kama wani matashi dan shekara 17 da ya yi wa yara ’yan shekara 5 da 7 fyade a yankin Nasarawa Jahun na jihar Bauchi.

Har ila yau, an kama wani mutum da ake zargin ya yi wa diyar makwabcinsa, yar shekara 8 fyade.