Ma’aikatan wucin-gadi dubu 13 da 970 Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Jihar Jigawa ta dauka aikin zaben da za a fara gudanarwa a gobe Asabar.
Shugaban Hukumar INEC a Jihar Dokta Mahmud Isah ya tabbatar da haka a wani taron manema labarai da hukumar ta kira a shekaranjiya Laraba a ofishinsa.
Ya ce kimanin mutum dubu 60 ne suka nemi aikin zaben amma gaba dayan wadanda hukumar ta dauka ba su kai mutane dubu ashirin ba.
Ya musanta jita-jitar da ake bazawa, cewa wadansu daga cikin ma’aikatan hukumar ne suka yi kama-karya wajen ba da sunayen wadanda za su yi aikin zaben. Ya ce hakan ba gaskiya ba ne.
Ya kara da cewa sun tanadi ma’aikatan tsaro a daukacin kananan hukumomin jihar da za su bai wa ma’aikatan zaben da kayan zaben kariya kafin da kuma lokacin zaben da kuma bayan an kammala.