✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa ku yi hattara da mayaudara – Allah Wahid

Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Ganyen Shayi na Ataye ta Jihar Katsina Alhaji Muntari Allah Wahid ya yi kira ga matasa su yi hattara da…

Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Ganyen Shayi na Ataye ta Jihar Katsina Alhaji Muntari Allah Wahid ya yi kira ga matasa su yi hattara da mayaudaran ’yan siyasa don kada su bata rayuwarsu nan gaba. Shugaban ya yi wannan kira ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishinsa da ke cikin garin Katsina. Ya ce, “Kowane lokaci ana cewa matasa su ne manyan gobe kuma shugabannin gobe amma abin takaici sai ake amfani da su ana tayar da tarzoma musamman a lokacin da zabe ya zo. “Da su ne ake amfani ana yin magudin zabe ta hanyar sanya su su sato akwatin zabe ko tayar da tarzoma lokacin zaben don samun damar dangwala wa wata jam’iyya ta samu nasara, ana ba su wasu ’yan kudin da ba su taka kara sun karya ba. Sannan da zarar wadanda suka yi amfana da su suka samu nasara, shi ke nan sun yi watsi da su sai kuma in irin wannan lokaci ya zo,” inji shi. Ya koka kan yadda ake amfani da kungiyoyin matasa da ake kakkafawa a duk lokacin da wani zabe ya karato.

Alhaji Muntari, ya yi kira ga matasan da su guji mu’mala da miyagun kwayoyi domin su ne ke batar musu da hankali suna aikata wasu ayyukan assha. “Mu tuna, bam u da kasar da ta fi Najeriya. Kuma inda ba a tanadin gobe da magabatanmu ba su yi mana tanadin da muke amfana da shi a yanzu ba duk kuwa da kokarin da ake yi na son mayar da mu bayi. Saboda haka, ina kira da babbar murya ga jama’ar kasar nan musamman matasa, su yi kokari su ba marada kunya tun daga wannan zaben da yake gudana domin nunawa duniya cewa mun waye, don haka mu ba da kyakkyawan misali tun daga yanzu wajen yin zaben cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya da lumana”, inji shi.