✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun gudanar da zanga-zangar goyon bayan SARS a Kano

A yi wa runduar kwaskwarima maimakon yin fatali da ita gaba daya.

Daruruwan matasa a jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna goyon bayan rundunar tsaro ta SARS wacce aka maye gurbinta da SWAT.

Sun yi zanga-zangar ne domin neman a yi wa runduar kwaskwarima maimakon yin fatali da ita gaba daya kamar yadda Babban Sufeton ‘Yan Najeriya Mohammed Adamu ya sanar a kwanan nan.

Matasan dai karkashin wata kungiya mai suna Inuwar Matasan Kano sun yi tattaki daga Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar har zuwa gidan gwamnati dauke da alluna da kwalaye suna kira ga Shugaban Kasa da Babban Sufeton ‘Yan Sandan kan su sake duba matsayinsu kan dakatar da rundunar ta SARS.

Matasan yayin da suke gudanar da zanga-zangar a kofar gidan gwamnati

Zanga-zangar dai a ta bakin jagoran matasan, Sunusi Khalid sun shirya ta ne domin aikewa gwamnatin tarayya da sako cewa rundunar kwaskwarima take bukata ba rushewa ba.

Da yake jawabi ga cincirindon matasan, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya godewa matasan kan abinda ya kira hangen nesan su tare da alkawarin mika bukatunsu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin dubawa.

Matasan na gudanar da zanga-zangar a kofar gidan gwamnati
Matasan na gudanar da zanga-zangar a kofar gidan gwamnati

Ya ce, “A ‘yan kwanakin nan, an yi ta samun zanga-zanga nan da can suna kira da a rushe SARS. Amma idan muka ci gaba da la’antar ‘yan sanda, shin zai yuwu mu zauna lafiya?

“Abinda tsarin yake bukata shine gyaran fuska domin a fitar da bata gari daga cikin ‘yan sandan amma ba wai rushewa ba. Wannan zanga-zanga abu ne da ya dace.” inji Ganduje.

Matasan na gudanar da zanga-zangar a kofar gidan gwamnati

Gwamnan ya kuma godewa matasan saboda shirya zanga-zangar ta lumana, yana mai jaddada muhimmancin ‘yan sanda wajen samar da tsaro da zaman lafiya.

Masu zanga-zangar dai sun rika daga kwalaye da alluna masu dauke da rubuce-rubuce kamar, “Muna goyon bayan SARS”, “A yi wa SARS gyaran fuska”, “Ba ma goyon bayan rushe SARS”, “Muna godiya ga IGP saboda gyara SARS”, da dai sauransu.