✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun yi garkuwa da yaro sun ba shi kwaya ya mutu

Wasu matasa masu shekaru 18 zuwa 20 sun yi garkuwa da yaro dan shekara 5 inda suka nemi iyayensa su biya kudin fansa Naira miliyan…

Wasu matasa masu shekaru 18 zuwa 20 sun yi garkuwa da yaro dan shekara 5 inda suka nemi iyayensa su biya kudin fansa Naira miliyan 50, kafin daga bisani su rage kudin zuwa Naira dubu 100.

Daya daga cikin ‘yan matasan mai suna Ibrahim Ahmad dan shekara 20 ya shaida wa manema labarai cewa, dan uwansa ne yaron da suka yi garkuwar da shi ya ce shi ne ya dauko shi daga makarantar Nazare ya mikashi a hannun abokan ta’asar na shi, “Ni ban shiga gidan da aka boye shi ba don gudun kada ya gane ni, da suka boye shi sun ba shi kwaya a lemon kwalba sai suka rufe masa baki da salatef,  da suka dawo suka tarar da shi a mace sai suka haka rami suka saka shi” in ji shi.

Gawar yaron wanda aka rufewa baki a lokacin da ‘yan sanda suka gano ta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Ahmed Iliyasu wanda ya jagoranci jami’an ‘yan sandan wajen gano gawar yaron ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya abku ne a a unguwar Karkasara a jihar Kano inda mahaifin yaron mai suna Ado Muhammad suka shaida wa rundunar an yi garkuwa da yaron daga makarantar Nazare da Firamare ta Ma’ahad da ke Karkasar  kana masu garkuwar sun nemi a basu kudin fansa Naira dubu 50,  nan take rundunar mu ta tsunduma cikin aiki muka gano wadanda ake zargin ta hanyar amfani da bayanan sirri da kimiyar zamani, kamar yadda babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya bamu umarni ko kadan ba zamu saurarawa batagari ba”. In ji shi Kwamishinan ‘yan sanda Ahmed Iliyasu.

Kwamishinan ‘yan sandan Kano Ahmad Iliyasu a lokacin da yake wa manema labarai karin haske