✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun zargi jami’an KASTELEA da haddasa hadari a Kaduna

Jami’an tsaro da suka hada da ‘Yan Sanda da sojoji da na jami’in tsaro na Hukumar Kula da Tsaro ta Fararen Hula (NSCDC) sun tarwatsa…

Jami’an tsaro da suka hada da ‘Yan Sanda da sojoji da na jami’in tsaro na Hukumar Kula da Tsaro ta Fararen Hula (NSCDC) sun tarwatsa dandazon wasu matasa da ke zanga-zanga nuna fushinsu saboda wani hadarin mota da wasu jami’an kula da masu ababen hawa na KASTELEA suka janyo akan titin Nnamdi Azikwe da ke cikin garin Kaduna.

Wakilinmu wanda ya ziyarci inda abin ya faru ya tarar da dandazon matasan wadanda suka tare titin domin nuna fushinsu tare da neman sai an biya motar bas din da talalace a sanadiyar hadarin da ya auku.

A cewarsu, jami’an na KASTELEA ne suka janyo hadarin saboda direban motar da suka tsayar ya ki tsayawa sai suka rika kokawar kwace sitiyarin motar daga hannunsa wanda hakan yasa motar ta kwace ta kuma fada cikin rami a gefen titi.

Aminiya ta samu bayani cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar yau Laraban nan wanda hakan ya sa akasarin fasinjoji da ke cikin motar suka jikkata.

“Ba’a rasa rai ba amma dai kam sun jikkata domin sai da aka rika fito da su daya bayan daga  cikin motar wacce ta fada cikin wani babban rami”.

“Kai dai Allah ne kawai ya kiyaye. Akwai bukatar dai a ja kunnen ma’aikatan KASTELEA su fahinci idan direba ya nemi guduwa bayan sun tsayar da shi su rabu da shi kawai,” in ji wani da abin ya auku a gabansa.

” Mu abinda muke bukata kawai anan shi ne gwamnati ko shugabanin KASTELEA dole ne su biya direban kudin motarsa in ba haka ba kuwa ba za’a bar hanyar ba,” in ji wani direban mota da ke wajen.

Daga bisani dole jami’an tsaro suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa matasan wadanda suka fara jifan ‘yan Sandan su kuma suka maida martani da barkonon tsohuwa.

An dai samu tarwatsa matasan bayan an karo yawan jami’an tsaro wajen bayan manyan jami’an tsaro da shugaban karamar hukumar Kaduna ta Kudu sun halarci wajen domin ganin an maido da doka da oda.

Aminiya ta samu bayani cewa jami’an na KASTELEA da aka zarga da janyo hatsarin sun gudu sun bar motarsu a wajen.