✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan APC sun yi garkuwa da ’yan majalisa uku a Kaduna

A yayin da wutar rikicin Jam’iyyar APC ke ci gaba da ruruwa a Jihar Kaduna, wasu matasan jam’iyyar sun yi garkuwa da wasu ’yan majalisa…

A yayin da wutar rikicin Jam’iyyar APC ke ci gaba da ruruwa a Jihar Kaduna, wasu matasan jam’iyyar sun yi garkuwa da wasu ’yan majalisa na tsawon wasu sa’o’i.
Matasan sun yi garkuwa da ’yan majalisar ne a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na wasu kananan hukumomi uku.
Kananan hukumomin su ne Kaduna ta Kudu da Kaduna ta Arewa sai kuma karamar Hukumar Igabi. Taron a cewar majiyarmu ya samu halartar ’yan majalisa uku daga wadannan kananan hukumomi.
Gwamnar Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya kira taron a matsayinsa na mai shiga tsakani domin sulhunta bangarorin da ke rikici da juna a jam’iyyar, bayan zaben shugabannin jam’iyyar na gundumomi da aka yi fiye da mako biyu da suka wuce.
Aminiya ta jiyo cewa taron da aka shirya yin sa da misalin karfe 10 na safe a masaukin Gwamnan da ke titin Sultan a Kaduna bai yiwu ba saboda rikicin da matasan suka tayar a kofar shiga cikin gidan inda suka rika fadin miyagun kalamai ga ’yan majalisun da ke cikin dakin taron.
Matasan sun rika cewa duk dan majalisar da ya fito daga cikin gidan sai sun yi masa duka.
Wani dan jam’iyar da ya halarci taron da bai so a ambaci sunansa, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce ko shakka babu, matasan sun nemi cin zarafin mutanen da ke wurin.
“Matasan sun zo wurin taron ne da nufin nuna bacin ransu kan yadda aka kasa fadin sunayen wadanda suka ci zaben shugabannin jam’iyyar da aka yi kwanaki kusan 18. Wannan ya sa suka bukaci da a tabbatar da adalci wajen fitar da sakamakon zaben, kuma a yayin haka ne suka yi garkuwa da wasu ’yan majalisa da ke wurin da suka hada da Barista Ibrahim Sani Mai wakiltar karamar Hukumar Igabi a Majalisar Wakilai da Alhaji Rufa’i Chanchangi mai wakiltar Kaduna ta Kudu. Sai Bala Yunusa shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna,” inji shi.
Duk kokarin Gwamna Kwankwaso don ganin an ba ’yan jam’iyyar hakuri don a samu damar yin taron ya ci tura, wanda hakan ya sa ya fice daga cikin gidan ya yi tafiyarsa.
Su kuma ’yan majalisar da ke cikin gidan tare da shi, sai suka zauna a ciki domin tsoron abin da ka iya faruwa da su idan sun fito, yayin da matasan suka ce babu inda za su kuma duk wanda ya fito waje sai sun buge shi.
Daga baya ’yan majalisar sun fice daga gidan bayan an karkatar da hankalin matasan cewa babu kowa a cikin gidan domin sun rigaya sun bi tawagar Gwamnan Kano.