✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan Jihar Nasarawa sun nemi ’yan majalisa su guji tozarta Gwamna Al-Makura

kungiyoyin matasa a Jihar Nasarawa sun yi kiran a samun fahimtar juna a tsakanin banagren zartarwa da na majalisar dokokin jihar domin samun zaman lafiya…

Gwamnan Umaru Tanko Al-Makura na Jihar Nasarawakungiyoyin matasa a Jihar Nasarawa sun yi kiran a samun fahimtar juna a tsakanin banagren zartarwa da na majalisar dokokin jihar domin samun zaman lafiya da ci gaba mai ma’ana a jihar. Shugabannin kungiyoyin matasan Jam’iyyar APC da na PDP a jihar ne suka yi wannan kira a wani zantawa da suka yi da manema labarai a Lafiya a karshen makon jiya. Matasan sun yi kira ga ’yan majalisar su maida hankali wajen gudanar da ayyukan da suka shafi ci gaban jama’a maimakon su rika sa baki cikin harkoki da ba su shafi jama’a ba.
Shugaban kungiyar sa-kai na Ta’al (Ta’al boluntary Group) na jihar Baba Osama wanda ya fara jawabi ya ce “A duk lokacin da aka kammala zabe, ya kamata ’yan siyasa su rika kawar da bambancin jam’iyyunsu, su hada kai domin ci gaban jihar baki daya.” Ya ce akwai matsaloli da dama da jama’ar Jihar Nasarawa suke fuskanta a yanzu da suka hada da rashin tallafi ga dalibai da rashin aikin yi ga wadanda suka kammala karatu da sauransu da ya kamata ’yan majalisa su mayar da hankali a kansu maimakon su rika yin abin da bai da tushe ko amfani ga jama’a.
A jawabin daya daga cikin shugabannin matasan PDP a jihar Muhammed Laminu ya ce lokaci ya yi da ’yan siyasa musamman ’yan majalisar jihar za su daina nuna bambancin siyasa da kabilanci su mayar da hankali kan abubuwan da za su kawo ci gaban jihar. Ya ce “Ina kira ga ’yan siyasa musamman ’yan majalisa su yi la’akari da kudirorin gwamnati mai ci a karkashin Gwamna Umaru Al-Makura na kawo canji mai ma’ana a fannonin rayuwar al’ummar jihar, su hada kai da shi don samun zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.”
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne majalisar ta ba da umurnin a canja sunan makarantar zamani da gwamnatin jihar ta gina a Lafiya da ake kira Ta’al Model Primary, Nursery and Junior Secondary School da sauran kaddarorin gwamnatin jihar da aka sanya sunan Gwamnan. Majalisar ta kuma nemi a cire mai ba Gwamnan shawara kan harkokin jam’iyyu Hajiya Hajarat Ibrahim danyaro lamarin ya sa kungiyoyin matasa da dama suka hallara a Lafiya inda suka yi kira ga ’yan majalisar su maida hankali ga ayyukan da suka shafi ci gaban jama’a a mazabunsu.