✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan Shuwa-Arab sun yunkuro don farfado da al’adunsu

kungiyar Matasan Harshen Shuwa-Arab mai suna Arab-Shuwa Youth Forum sun yi taron don farfado da al’adunsu.kungiyar ta yi taron ne mai suna ‘Fadakar da Al’umma…

kungiyar Matasan Harshen Shuwa-Arab mai suna Arab-Shuwa Youth Forum sun yi taron don farfado da al’adunsu.
kungiyar ta yi taron ne mai suna ‘Fadakar da Al’umma muhimmancin al’ada’ a Legas a ranar Lahadi.
Shugaban kungiyar, Goni Dauda ya bayyana wa Aminiya bayan an kammala taron cewa ya zama dole su kira taron ne saboda kalubalen da yaren Shuwa yake fuskanta.
Ya ce “Idan ka duba za ka ga mutanenmu suna jin kunyar su bayyana cewa su ’yan shuwa ne. Misali idan ka duba a Legas za ka cewa akwai mutanenmu da suke kiran kansu Yarabawa. Ba sa son a kira su Shuwa-Arab. Akwai wadanda ko yaren ma ba sa ji sai dai Yarabanci da Turanci. Ba a zancen al’adunmu na gargajiya. Ba su san su ba. Ka ga ke nan idan ba mu tashi tsaye ba, nan gaba yarenmu da al’adunmu za su shiga wani hali.”
Ya ci gaba da cewa: “Shi ya sa muka ga ya dace mu kafa kungiyar da za ta fadakar da al’ummarmu muhimmancin riko da al’adunmu na gargajiya ta yadda da zarar an ga dan Shuwa za a gane shi ba tare da wata matsala ba. Haka zalika muna son mutanenmu su fahimci muhimmacin ilimin ’ya’ya maza da mata na boko da na addini.”
Da yake jawabi a wurin taron, Sarkin Shuwa-Arab na Jihar Legas, Sultan Isa Sa’id ya yaba wa matasan kan yunkurin da suka yi na dawo da martabar harshen Shuwa da al’adunsu na gargajiya.
Ya bukaci ’yan Shuwa su fahimci muhimmanci hadin kai don shi zai kai su gaci.
Ya nemi shugabannin kungiyar su yi hakuri da nauyin da aka dora musu kuma su yi aiki tukuru don ganin kungiyar ta cimma burin da ta sa gaba.
Sarkin ya jaddada goyon bayansa ga yunkurin da matasan suka yi inda ya ce babbar nasara ce ga al’ummar Shuwa baki daya.
Shugaban shirye-shirye na kasa na kungiyar, Sa’id Isa ya yi kira ga daukacin Shuwa su rika sanya ’ya’yansu a makarantar boko da ta Islamiyya.
“Ilimi shi ne gishirin zaman duniya, idan babu ilimi al’umma ta shiga garari. Ina kira ga iyayenmu su rika sanya ’ya’yansu a makaranta don su samu ilimin boko da na addini. Wannan shi zai sa su san ’yancinsu kuma su kwato hakkinsu da aka danne.” Inji shi.
Ya bayyana cewa rashin ilimi shi ne yake dakile ci gaban al’ummar shuwa.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar Arewa United Gamji Association na Jihar Legas, Alhaji Garba Tudu ya bukaci matasan Shuwa su hada kai don cimma burin da suka sa a gaba.
Ya bukaci ’yan Arewa su yi riko da al’adunsu na gargajiya don kada wasu bakin al’adu su mamaye su.