✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan Wudil sun karrama tsohon kwamishina

Matasan Karamar Hukumar Wudil da ke Jihar Kano sun karrama tsohon Kwamishinan Ayyuka da Gidaje na Jihar, Injiniya Aminu Aliyu Wudil a karshen makon jiya.…

Matasan Karamar Hukumar Wudil da ke Jihar Kano sun karrama tsohon Kwamishinan Ayyuka da Gidaje na Jihar, Injiniya Aminu Aliyu Wudil a karshen makon jiya.

Gamayyar Matasan a karkashin jagorancin Malam Ya’u Ado Wudil sun ce sun karrama tsohon kwamishinan ne domin irin gudunmawar da bayar wajen ci gaban karamar hukumar da jihar baki dayanta. Ya ce hakika su al’ummar Wudil ba su da abin fadi ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje domin ba wa namu damar wakiltar jama’a a matsayin kwamishina kuma ya kammala, wanda shi ne dalilin shirya wannan taro da a iya cewa shi ne irinsa na farko a karamar hukumar don taya shi murnar kammala aikinsa na kwamishina lafiya.

Malam Ya’u ya kara da cewa duk wanda Allah Ya ba shi matsayi kuma ya gama lafiya, akwai bukatar ’yan uwa da abokan arziki su taya shi murna. “Kuma muna kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sake duban al’ummar Wudil ya sake nada Injiniya Aminu Aliyu a matsayin kwamishina a karo na biyu, domin irin kwazonsa da sadaukar da kai da kuma taimaka wa al’umma,” inji shi. Ya tabo irin ayyukan da ya yi a matsayinsa na kwamishina.

A jawabin tsohon Kwamishinan Ayyuka da Gidaje Injiniya Aminu Aliyu ya gode wa wadanda suka shirya taron, ya ce hakika wannan ba karamin karamci ba ne aka yi masa. Ya ce da hadin kan al’umma ya cimma duk nasarorin da ya samu a wannan matsayi na kwamishina da ya rike ma’aikatu biyu, wanda shi ne mutum na farko a tarihin Jihar Kano da ya taba rike wadannan mukamai na Kwamishinan Ayyuka da Gidaje ga kuma Ma’aikatar Ilimi.

Injiniya Aminu Wudil ya bayyana  nasarorin da ya cimma da suka hada da gina gadajen sama da kuma hanyar kasa da shirin “Karkara Kalkal” da sauran ayyuka masu yawa. Ya ce duk ya samu wadannan nasarori ne bisa damar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya ba shi.

Jama’a da dama sun yi tsokaci kan irin ayyukan alherin da tsohon kwamishinan ya yi da kuma daukar ’yan asalin karamar hukumar a aiki da samar musu da guraben karatu da tallafa wa jama’a da sauransu. Kuma sun yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sake nada Injiniya Aminu Aliyu Wudil a mukamin kwamishina.