✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kai karar mahaifiyarsa kan korarsa daga gidanta

Da farko nayi murnar kasancewa tare da ni don na taimake shi, amma daga baya sai ya sauya rayuwarsa.

Wani matashi mai shekara 30 dan kasar Mexico ya kai karar mahaifiyarsa ga hukumomin kasar, saboda korarsa da ta yi daga gidanta kan ya gaza samun aiki kuma ba ya taimaka wa gidan da komai.

A Larabar makon da ya gabata ce kafafen watsa labarai na Mexico suka wallafa rahoton karar da matashin mai suna Christian Uriel, ya kai mahaifiyarsa da ’yar uwar mahaifiyar a ofishin shigar da korafi na kasar Mexico saboda zargin wulakanta shi da suka yi.

Bayan shigar da karar da Christian Uriel ya yi, ya bayyana cewa, sai da iyayen nasa suka lakada masa duka sannan suka kore shi daga gidan tare da watsa masa ruwa a jiki.

Sai dai abin da bai bayyana wa hukumomin ba shi ne, ya yi watanni a gidan mahaifiyar tasa kyauta ba tare da yana biyan komai ba, kuma bai taimaka da kudi a harkokin ’yan uwansa ko gudunmawa ga ’yan uwansa ba.

Mahaifiyar Christian ta bayyana cewa, danta ya kasance tare da ita tun farkon sanarwar barkewar annobar Covid-19, bayan ya rasa aikinsa.

Ta ce da farko tayi murnar kasancewarsa tare da ita don ta taimake shi, amma bayan wata hudu, sai Christian ya sauya rayuwarsa ta hanyar yini yana wasan ‘Video Games’, ba ya taimakon kowa sai da a girka abinci a kawo masa yana zaune.

Bayan kasar Mexico ta janye dokar hana fita da aka sanya, wasu wuraren kasuwanci sun bude harkokinsu, sai dai mahaifiyar matashin ta bukaci ya nemi aikin yi don ba da tasa gudunmawar ga gidan, amma ya yi watsi da batun, ya koma ko motsa jikinsa bai yi sai dai ya kwanta a gida kawai.

Wannan dabi’a da Christian ya dauka ta sa mahaifiyar ta kira ’yar uwarta don korarsa daga gida tare da watsa masa ruwa da kuma bugunsa da tsintsiya.

Jaridar Medico El Comercio ta wallafa tsokacin da Christian Uriel ya yi game da abin da mahaifiyarsa ta yi masa, don haka ya shigar da karar neman hakkinsa.

Nan gaba kadan kotu za ta zauna don yanke hukuncin kan karar da aka shigar gabanta.