Da Dumi Dumi

Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da wuka a Nasarawa

Wani matashi mai shekara 23, mai suna Ahmed Abdullahi, a unguwar Agyaragu da ke yankin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa, ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da wuka a safiyar yau Asabar.

Wani ganau ya bayyanawa Aminiya cewa, Ahmed ya yanka makogoron kishiyar mahaifiyarsa ne da wukar kicin wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa ranta.

Wakilinmu ya gano cewa, ‘yan’yan matar da aka kashe sun rike makamai don neman Ahmed su dau fansa game da kisan mahaifiyar su.

Jami’in hulda jama’a na rundunar ‘yan sanda ASP Ramhan Nansel, ya ce a yanzu haka sun kama Ahmed kuma suna ci gaba da bincike.

 

ADVERTISEMENT
Share