Daily Trust Aminiya - Matashi ya kashe Mahaifinsa bayan daba masa wuka a Kano
Subscribe

Matashi ya kashe Mahaifinsa bayan daba masa wuka a Kano

Rundunar ‘Yan sandan jihar Kano ta ce, ta kama wani matashi mai suna Habibu Ibrahim, da ke garin Asada a Karamar hukumar Doguwa, bisa laifin kashe mahaifinsa Malam Ibrahim Salihu mai kimanin shekaru 80, ta hanyar daba masa wuka a ciki.

Dan uwan Habibu, Yahaya Ibrahim ne ya sanarwa da ofishin ‘yan sandan Asada Doguwa, ranar 15 ga watan Satumba 2019.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka inda ya ce tuni suka garzaya da shi asibiti inda ya mutu yayin da ake kokarin ceto rayuwarshi.

DSP Abdullahi, ya kara da cewa matashin ya kashe mahaifin nasa ne sakamakon shaye-shaye da yake, wanda ya kaishi ga aikata wannan mummnan laifi. Ya ce, tuni hukumar tayi awon gaba da matashin domin ya girbi abin da ya shuka.

texem
More Stories