✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya rasa ransa a hannun masu adawa da tarbiyya

A Talatar da ta gabata wani matashi mai suna Aliyu Badamasi da ke zaune a garin Ramin Kura, a Karamar Hukumar Lere na Jihar Kaduna,…

A Talatar da ta gabata wani matashi mai suna Aliyu Badamasi da ke zaune a garin Ramin Kura, a Karamar Hukumar Lere na Jihar Kaduna, ya rasa ransa a hannun wasu matasa da suke adawa da ayyukan wata kungiya da ke yaki da rashin tarbiyyar da matasa ke yi da suka shafi munanan aski da sutura da shaye-shaye a garin.

Shi dai wannan matashi ya rasa ransa ne a lokacin ya fito daga gidansu don kiran yayansa, mai suna Abdurrahaman Badamasi wanda dan wannan kungiya ne, lokacin da wadannan matasa masu adawa da hana munanan aski suka far masa da duka, lamarin da ya kai ga daya  daga cikin matasan mai suna Maharazu Habu ya cakawa marigayi Aliyu Badamasi makami a makoshi, inda ya mutu nan take.

Da yake yi wa wakilinmu karin bayani kan yadda  al’amari ya faru, wani kawun marigayin da aka yi abin kan idonsa, mai suna Malam Imrana Mu’azu Ramin Kura, ya bayyana cewa ainihin abin da ya faru shi ne akwai wata kungiya da aka kafa a wannan gari, wacce ke koyawa matasa tarbiyya tare da yaki da mummunan aski da sanya suturar fitsara da kuma shaye-shaye da matasa ke yi.

Ya ce “sai wadansu yaran wannan gari guda 22, da suke aikata irin wadannan miyagun dabi’u suka yi zanga-zanga kan nuna rashin amince da kungiyar, kuma kungiyar ta kama mutum 11 daga cikin wadannan matasa, aka yi wa kowannesu hukuncin  bulala 10 tare da yi masu aski.

“To akwai wani mutum da yake daurewa yaransa gindi, a wannan gari, wanda akwai yaronsa mai suna Naziru Habu da yake cikin yaran da suka yi zanga-zanga,” Inji shi.

Ya kuma kara da cewa, “to wannan mutum shi ne ake zargin ya turo yaransa zuwa gidan su marigayin don su bugi ‘ya’yan marigayin mai suna Abdurrahaman Badamasi wanda dan wannan kungiya ne. Shi kuma marigayin yana tare da mahaifinsa mai suna  Badamasi Yakubu  a cikin gida, sai mahaifin ya ce ya tashi ya je waje ya dubo wane hayaniya ake, kila yaran wannan mutumin ne da ya ce zai turo su daki Abdurrahaman, ya ce masa ya dawo gida. To da marigayin ya fito sai  ya sami wadannan yara ne da ake magana, suna ta dukan  yayan nasa Abdurhaman, sai marigayin ya shiga fadan,” a cewarsa.

Malam Imrana ya kara da cewa “a cikin wadannan yara akwai wani mai suna Maharazu Habu sai ya fada gida a guje, ya dauko wani makami ya cakawa marigayin a makoshi. Ganin sai na kai masa kamu, amma sai na zame na fadi, shi kuma ya ruga cikin gida na bishi, ban sami kama shi ba, ya gudu. Daga nan muka dauki Aliyu muka tafi da shi asibiti, inda ya rasu”.

Ya ce marigayi Aliyu babu ruwansa da wannan magana, mahaifinsu ne ya aike shi ya kirawo yayansa Abdurrahaman dan wannan kungiya,  daga nan ajalinsa ya zo a wajen, aka caka masa makamin  da ya yi sanadin rasuwarsa. Ya ce a rayuwarsa bai taba ganin irin wannan ta’adanci ba, don  haka duk lokacin da ya tuna wannan abu, sai hawaye sun zubo masa.

Shi ma a zantawarsa da da wakilinmu, Sarkin garin Ramin Kura, Alhaji Musa Idris ya bayyana cewa gaskiya ba su ji dadin faruwar wannan al’amari ba. Saboda ayyukan alherin da kungiyar take yi a  garin. Ya ce su ne suka kafa kungiyar domin ganin kowa ya zama mai tarbiyya da ladabi, kuma kowa yarda da haka a garin.

Ya ce amma daga baya sai wannan mutum mai daurewa ‘ya’yansa gindi, ya ce ‘ya’yansa ba zasu bi dokokin kungiyar ba. Sarkin ya yi bayanin cewa kungiyar zata cigaba da ayyukanta, domin yara da dama sun sami tarbiyya sakamakon ayyukan kungiyar masamman wajen hana shaye-shayen miyagun kwayoyi da askin banza da sanya sutura marasa kyau.

Kakakin Hukumar ‘yan sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce ya zuwa yanzu wannan magana tana hanun Jami’an binciken aikata manyan laifuffuka na rundunar, kuma da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da wadanda aka samu da laifi a gaban kotu don fuskantar.