✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya rataye kansa a Bakori jihar Katsina

Wani matashi mai suna Badamasi Alhaji Musa ya rataye kansa a wata bishiyar mangoro wanda hakan yasa ya rasa ransa. Wannan al’amari ya faru a…

Wani matashi mai suna Badamasi Alhaji Musa ya rataye kansa a wata bishiyar mangoro wanda hakan yasa ya rasa ransa.

Wannan al’amari ya faru a garin Kabomo da ke cikin Karamar hukumar Bakori a Jahar Katsina a ranar Talata da misalin karfe 10 na safe.

Kamar yadda aka ce, Badamasi na fama da matsalar tabin hankali. Tuni dai Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina Sufurtanda Gambo Isa, ya tabbatar da faruwar lamarin, sannan ya kara da cewa, tuni aka dauki gawar zuwa asibiti a garin Bakori don yin bincike. Kazalika, ya ce, rundunar su na ci gaba da binciken lamarin.