Da Dumi Dumi

Matashi ya rataye kansa ya mutu a Kano

Wani Matashi mai suna Nasiru Ali Abdussalam da ke unguwar Sheka a Karamar hukumar Kumbotso, ya rataye kansa ya mutu bisa wani dalili da har yanzu ba a gano ba.

An gano gawar Nasiru, ne a rataye a jikin rufin dakinsa, bayan da abokan kasuwancinsa suka zo karbar kayan gini da suka siya a hannunsa.

Rahotanni sun bayyana cewa, Nasiru ya yanke shawarar rataye kansa ne sakamakon yana son yin aure amma Mahaifiyarshi ta hana.

Sai dai mahaifiyar Marigayin, Malama Amina Umar Ahmad, ta bayyanawa majiyarmu cewa, kwananki kadan kafin rasuwar tasa, alamu sun nuna Nasiru yana cikin damuwa, har takai ga yana cewa, “Rayuwar nan wanda ya mutu ya huta da matsalolin duniyar nan.” Sai dai mahaifiyar ta musanta zargin cewa, Nasiru ya rataye kansa ne sakamakon ta hana shi aure.

ADVERTISEMENT
Share