✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya sace yaron shekara 7 yana neman a biya Naira milyan 3.5

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta yi nasarar kame wani matashi mai shekara 19 a rukunin gigaje na Gabukka da ke cikin birnin Gombe, akan…

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta yi nasarar kame wani matashi mai shekara 19 a rukunin gigaje na Gabukka da ke cikin birnin Gombe, akan tuhumarsa da laifin yin garkuwa da yaro dan shekara bakwai wanda aka sakaya sunansa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan (SARS) na jihar SP Obed Mary Malum, ya ce wanda ake tuhumar mai suna Mohammed Sani Ahmad, an kama shi ranar 23 ga Satumba 2019 kwana uku da iyayen yaron suka sanar da bacewar dan nasu.

Mohammed Sani, ya dauke yaron ne a ranar Juma’a 20 ga Satumba 2019 a masallacin Kumbiya-Kumbiya lokacin da yaron yake alwala.

Matashin ya kira mahaifin yaron mai suna Malam Abubakar, inda ya bukaci a biya kudin fansar yaron har Naira Miliyan 3.5.