Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Matashi ya sare dan yatsarsa saboda kuskuren zaben wata jam’iyya a Indiya

Wani matashi mai shekara 25 dan kasar Indiya ya sare yatsarsa bayan ya yi kukuren zaben wata jam’iyya daban a babban zaben kasar da aka yi.

Matashin mai suna Pawan Kumar ya rude lokacin da ya je gaban na’urar zabe mai amfani da lantarki inda ya zabi Jam’iyyar Narendra Modi, maimakon ya zabi jam’iyyar adawa a Jihar Uttar Pradesh da ke Arewacin Indiya, inji dan uwan Pawan.

ADVERTISEMENT

Nadamar zaben jam’iyyar ya sa Pawan Kumar, ya koma gida ya samu wukar ya datse yatsar.

Duk da yake ana kada kuri’a ne ta hanyar amfani da na’urar lantarki a tashoshin zabe,  kowace yatsa da mai zabe ya kada kur’arsa ana shafa mata tawada a matsayin wanda ya kada kuri’arsa, don tabbatar da bai sake yin zabe sau biyu ba.

ADVERTISEMENT

Dan uwan Pawan, Kailash Chandra ya fada wa kafar sadarwa ta Agence France ta waya cewa, “Pawan Kumar ya yi murna sosai ganin cewa wannan shi ne zabensa na farko a duniya,” amma daga bisani ya gano kuskuren zaben da ya yi, sai ya je ya datse yatsar da ya kada kuri’ar da ita.

“A duk lokacin da ya kalli tawadar da aka shafa masa a yatsunsa, sai ya ji bacin rai,”inji Kailash

Kailash Chandra, ya ce iyalan Pawan sun kai shi asibiti, daga nan aka yi ta yada hoton bidiyon  da ke nuna mutum na farko mai kada kuri’a da yankakken yatsa.

A wani bidiyo Pawan yana cewa, “Na yi niyyar zaben jam’iyya mai alamar giwa amma sai na yi kuskuren zaben jam’iyya mai alamar fulawa a lokacin da na je kada kuri’a ba a matsanta min akan in zai wata jam’iyya ba, kuskure ne kawai.”